Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-26 17:13:32    
Gwamnatin kasar Sin tana bayar da 'yancin yin addinin da mutum ya ga dama

cri
Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malama Fatima Sada, wato mai sauraronmu daga birnin Zaria na jihar Kaduna ta tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ta aiko mana, ta ce, shin musulmin da ke kasar Sin ko miliyan nawa ne? ko gwamnatin kasar Sin tana bayar da 'yancin yin addinin da mutum ya ga dama? Sa'an nan shin ko addinin Buddah addinin gwamnati ne, watau addinin da gwamnati ta yarda a yi shi kadai? Hasali ma dai, kafin wannan, sauran masu sauraronmu ma sun taba yi mana irin wadannan tambayoyi. Sabo da haka, bari mu ba da amsa ga wadannan tambayoyin masu sauraronmu, ta yadda za mu kara fadakar da masu sauraro a kan halin da kasar Sin ke ciki a fannin addini.

Masu sauraro, kasar Sin kasa ce da ke da addinai da dama. Addinan da ake bi a nan kasar Sin sun hada da addinin Buddah da Taoism da musulunci da Katolika da kuma na kirista. Daga cikinsu, musulunci ya sami shigowa a nan kasar Sin a kimanin karni na bakwai, wato bisa 'yan kasuwa musulmi na kasashen yammacin Asiya da kuma gabashinta ta hanyar siliki. Addinin dai ya jima yana bunkasa, har ma ya yadu sosai a wurare daban daban na kasar Sin, kuma sannu a hankali ya zama addinin da kananan kabilun kasar Sin guda goma suke bi, ciki har da kabilar Hui da ta Weiwuer. A halin yanzu dai, akwai musulmi sama da miliyan 18 a nan kasar Sin, a yayin da ake iya samun masallatai kusan dubu 30 da kuma limamai sama da dubu 40.

Game da tambaya ta biyu da malama Fatima Sada ta yi mana, wato ko gwamnatin kasar Sin tana bayar da 'yancin yin addinin da mutum ya ga dama? Amsa ita ce, e, haka ne, 'yancin yin addinin da mutum ya ga dama wani muhimmin hakki ne na mutanen kasar Sin, wanda kuma yake samun karewa daga tsarin mulkin kasar Sin da kuma dokokin kasar. A bayyane ne tsarin mulkin jamhuriyar jama'ar kasar Sin ya tanadi cewa, 'Mutanen jamhuriyar jama'ar kasar Sin suna da 'yancin bin addinin da suka ga dama.' 'ko wace hukumar kasa ko kungiya ko mutum ba za su iya tilasta wa mutumin kasar da ya bi wani addini ko kuma kada ya bi wani addini ba, kuma an hana nuna bambanci tsakanin mutanen da suke bin addini da kuma wadanda ba su bi.' 'kasar Sin tana kiyaye bukukuwan addini wadanda ake yi kamar yadda ya kamata.' A sa'i daya kuma, tsarin mulkin ya kuma tanadi cewa, 'ko wane mutum ba zai iya yin amfani da addini wajen lahanta tsarin zaman al'umma da lalata lafiyar jikin jama'a da kuma kawo cikas ga tsarin ilmantarwa na kasar ba.' 'kungiyoyin addinai da harkokin addini tilas ne ba za su samu jagoranci daga rukunonin kasashen waje ba.'

Bayan haka, muna so mu kara muku bayani a kan ma'anar 'yancin mutanen kasar Sin na yin addinin da suka ga dama. Nufinsa shi ne, mutanen kasar Sin suna da 'yancin bin addini da kuma na kin yin addini. A sa'i daya kuma, suna da 'yancin yin wannan addini da na yin wancan addini. A cikin addini daya, suna da 'yancin bin wannan darika da kuma wata daban. Bayan haka kuma, watakila ba su yin addini a da, amma suna da 'yancin yin addini a yanzu, ko kuma da suna yin addini, amma yanzu suna da 'yancin daina yin addini. Wato ana girmama da kuma kiyaye 'yancin yin addini da kuma 'yanci na kin yin addini.

To, masu sauraro, ya zuwa yanzu, watakila kun riga kun sami amsa dangane da tambayar ko addinin Buddah addini ne da gwamnati ta yarda a yi shi kadai. Sabo da mun riga mun bayyana muku cewa, 'yancin yin addinin da mutum ya ga dama wani babban hakki ne na mutanen kasar Sin, wanda yake samun karewa daga tsarin mulkin kasar Sin da kuma dokokin kasar. Ban da wannan kuma, a kasar Sin, addinai iri daban daban daidai suke. Kome yawan mutanen da suke bin shi da kuma tasirin da yake bayarwa, daidai suke a gaban dokoki, babu wani addinin da yake da matsayin fifiko. Gwamnati ba ta nuna bambanci a tsakaninsu ba. (Lubabatu Lei)