Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-26 16:12:52    
Sojojin Isra'ila sun kai farmaki da boma bomai kan shiyyar da ke kudancin Lebanon, sakamakon haka 'yan sa ido 4 na M.D.D. suka rasa rayukansu

cri
Ran 25 ga wata da dare, sojojin Isra'ila sun kai farmaki da boma bomai kan wata tashar sa ido ta sojojin kiyaye zaman lafiya ta M.D.D. da ke kudancin kasar Lebanon, 'yan sa ido 4 na M.D.D.sun mutu, inda suka kunshe da Du Zhaoyu, wani mutumin kasar Sin.

Ran 26 ga wata, Mr. Liu Jianchao, kakakin ma'aiatar harkokin waje na kasar Sin ya yi jawabi cewa, bangaren Sin ya yi mamaki sosai kan wannan, kuma da kakkausan harshe ya yi allah wadai da al'amarin. Bangaren Sin ya nuna juyayi ga wadannan 'yan sa ido. Kasar Sin ta bukaci bangarorin da ke cikin rikicin da su tabbatar da kwanciyar hankali na 'yan kiyaye zaman lafiya na M.D.D., kuma ta karfafa yin kira ga bangarorin da suka tayar da rikici, da nan da nan su tsgaita bude wuta, kuma su komo teburin shawarwari, da kuma kan hanyar warware matsalar ta siyasa.

A wannan rana kuma, Mr. Zhaijuan, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin ya gana da Yehoyada Haim, jakadar kasar Isra'ila da ke kasar Sin cikin gaggawa. Mr. Zhaijuan ya bayyana cewa, shugabannin kasar Sin sun yi mamaki da bakin ciki kan mutuwar mutumi mai aikin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin. Bangaren Sin ya bukaci bangaren Isra'ila da ya yi bincike a duka fannoni. Mr. Yehoyada ya bayyana cewa, gwamnatin Isra'ila ta yi bakin ciki kan al'amarin, kuma za ta aiwatar da bincike a duk fannoni.

Bayan faruwar al'amarin, Kofi Annan, babban sakataren M.D.D. ya bayar da wata sanarwa, inda ya yi mamaki sosai kan farmakin da Isra'ila ta kai wa sansanin M.D.D. da ke kudancin kasar Lebanon, kuma ya bukaci sojojin Isra'ila da tilas ne su dakatar da farmaki kamar haka, da kuma yin bincike kan wannan. (Bilkisu)