An kawo karshen gasar cin kofin duniya ta 15 ta wasan tsunduma cikin ruwa a ran 23 ga watan da muke ciki a birnin Changshu dake gabashin kasar Sin, wadda aka shafe kwanaki 5 ana yinta, inda 'yan wasan kasar Sin suka kwashe dukanin lambobin zinariya. Gasar tsunduma cikin ruwa, wata gagarumar gasa ce da hadaddiyar kungiyar wasan iyo ta kasa da kasa takan shirya sau daya cikin shekaru bibbiyu.
An bude gasar cin kofin duniya ta 49 ta wasan harbe-harbe a ran 23 ga wata a birnin Zagreb, hedkwatar kasar Croatia. ' Yan wasa masu karewa a fannin harbe-harbe daga kasashe da jihohi 107 na duniya sun halarci gasar, wadda za a kammala a ran 6 ga watan gobe.
Kwanakin baya ba da dadewa ba, babbar hukumar kula da harkokin wasannin motsa jiki ta kasar Sin ta shelanta, cewa za a gudanar da taron wasannin motsa jiki kan ruwa na kasar Sin a karo na farko tun daga ran 28 ga watan Agusta zuwa ran 8 ga watan Satumba na shekara mai zuwa a birnin Ri Zhao dake bakin teku a kasar Sin. Manyan ire-iren wasanni guda 8 da kananan ire-irensu guda 110 sun hada da wasan tseren kwale-kwale masu filafilai, da wasan tseren kwale-kwale masu inji, da wasan tseren kananan kwale-kwale da kuma wasanin motsa jiki na wuce iyaka da dai sauransu. Wadanda za su laharci gasar sun hada da masu koyar da 'yan wasa, da alkalai da kuma 'yan wasa da yawansu ya wuce 3,300. An labarta, cewa za a yi irin wannan gasa sau daya cikin shekaru hudu.
A ran 23 ga wata, an yi karo na karshe cikin kungiyar A ta ta gasar cin kofin Asiya ta 15 ta wasan kwallon kafa na mata da ake yi a kasar Australiya, inda kungiyar kasar Sin ta sha kaye daga hannun 'yan wasan kasar Japan da ci sifiri da daya, wato ke nan ta zo ta biyu cikin kungiyar din ta A, kuma ta samu iznin shiga zagaye na uku. Za a kammala wannan gasa ne a ran 30 ga wata.
An kawo karshen gagarumar gasa ta 93 ta wasan tseren keke na zagaya kasar Faransa a ran 23 ga wata. Dan wasa mai suna Floyd Landis daga kasar Amurka ya zama zakara a gun gasar da sa'o'I 89 da minti 39 da dakika 30. Gasar nan, wata gagarumar gasa ce ta tseren keke kan hanyar mota ta tsawon kilomita 3,657 a Turai. ( Sani Wang )
|