Da farko za mu gabatar muku da wani labari dangane da kiwon lafiya, za mu gabatar da wasu shawarce-shawarce kan yadda za a yin rigakafin ciwon tibi yadda ya kamata, bayan haka kuma, za mu karanta muku da wani bayanin da ke da lakabi haka 'yin barci ta hanyar kimiyya zai kiwo lafiyar mutane'.
Yanzu za mu soma gabatar muku da labarin da muka shirya muku.
Ciwon tibi ya fi yaduwa a lokacin bazara. Masana sun tuna wa mutane da cewa, bin al'ada mai kyau a fannin kiwon lafiya ya zama abin tilas wajen yin rigakafin ciwon tibi, musamman ma kada a yi miyau duk inda aka ga dama.
Darektan cibiyar shawo kan ciwace-ciwace masu yaduwa ta jihar Xinjiang Mr. Gu Xiaoming ya bayyana cewa, ciwon tibi ciwo ne na hanyoyin numfashi na jukunan mutane, kwayoyin cutar tibi suna yaduwa ta hanyoyin yin tari da atishawa da kuma yin miyau, mai yiwuwa ne mutane za su kamu da wannan ciwo saboda sun yi numfashin feshin da ke kunshe da kwayoyin cutar tibi.
Saboda kwayoyin cutar tibi sun yi watanni 6 zuwa 8 suna kasancewa a cikin miyau maras laima, har ma, kwayoyin cutar sun yi kwanaki 8 zuwa 10 suna kasancewa a cikin iska, saboda haka, hana yin miyau a duk inda aka ga dama muhimmin mataki ne aka dauka don shawo kan ciwon tibi.
Ban da wannan kuma, Mr. Gu Xiaoming yana ganin cewa, ana bukatar kara daukan matakan da aka ambata a gaba don shawo kan ciwon tibi.
Da farko dai, an mai da hankali kan mutanen da suke fama da ciwon tibi, a gano masu kamu da wannan ciwo tun da wuri, a yi musu jiyya yadda ya kamata kuma tun da wuri. Mr. Gu ya yi bayanin cewa, rika yin tari da kuma yin miyau har tsawon kwanaki fiye da 3, ko kuma idan an gano jini a cikin miyaun da wani mutum ya yi, ana shakkar ko ya kamu da wannan ciwo, ya kamata ya je cibiyar shawo kan ciwace-ciwace na wurin don neman shawara daga likitoci da yin bincike da kuma shawo kan wannan ciwo; na biyu kuma shi ne, wajibi ne a kan bude tagogi don shigar da iska mai tsabta kullun, da kuma motsa jiki, ta yadda mutane za su kara karfin garkuwar jikunansu; na karshe kuma shi ne, kamata ya yi a yi allurar rigakafin ciwon tibi ga jarirai da kuma kananan yara cikin lokaci.(Tasallah)
|