Akwai wani karin magana da ake yi a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin da ke cewa, "duk wanda bai sa kafa a tsoffafin hanyoyi na birnin Beijing ba, to, ba zai san birnin Beijing ba, tamkar bai taba zuwa Beijing ba. Tsoffafin hanyoyi manya da kanana sun ratsa ko ina cikin duk tsohon gari na Beijing, tamkar jijiyoyin jikin mutum.
An ce, an fara shimfida tsoffafin hanyoyi a birnin Beijing ne, tun bayan da daular Yuan ta mayar da birnin Beijing da ya zama hedkwatar kasar Sin a karni na 13. 'Yan kabilar Mongoliya ne suka kafa daular Yuan a duk kasar Sin baki daya. Ya zuwa yanzu dai, ana kiran wadannan tsoffafin hanyoyi da sunan "HUTONG" a birnin Beijing, abin da ake nufin "HUTONG" cikin harshen Mongoliya shi ne "rijiya". Daidai ne, an shimfida tsofaffin hanyoyin nan ne bisa tsarin rijiyoyi da ke kasancewa a tsohon gari na Beijing tun can farko.
Yanzu, wadannan tsoffafin kananan hanyoyi sun riga sun zama wata alama ce ga al'adun gargajiyar birnin Beijing. Malam Li Mingde, masanin ilmin al'adun jama'ar Sin ya ce, daga sunayen tsoffafin hanyoyin nan daban daban, za a gano zaman rayuwar da 'yan birnin Beijing suka yi a wancan lokaci. Ya bayyana cewa, "akwai wata tsohuwar hanya da ake kira "Baihuashenchu" cikin Sinnanci a tsohon garin Beijing, "Baihuashengchu" sunan wani shahararren mutum ne wanda ya taba zama a wannan hanya a can can zamanin da."
Ya zuwa yanzu dai ma ba a canja sunan tsohuwar hanyar nan ba. Abin da ake nufin "Baihuashengchu" cikin Sinanci shi ne hanya mai nisa da ke da furanni iri-iri har dari.
Malam Li Mingde ya kara da cewa, akwai wata tsohuwar hanya da ake kira "Zhugan" cikin Sinanci, abin da ake nufin "Zhugang" shi ne "sandar gora". Dalilin da ya sa ake kira tsohuwar hanyar nan da wannan suna shi ne domin siffarta ta yi daidai da wata sandar gora.
Malam Kuang Han, kwararre ne a fannin zane-zane na kasar Sin wanda ya shahara wajen zanen tsoffafin hanyoyi, ko da yake an haife shi ne a kudancin kasar Sin, amma yana sha'awar tsoffafin hanyoyin birnin Beijing da ke a arewacin kasar Sin ainun. Da ya tabo magana a kan tsoffafin hanyoyin Beijing, sai ya ce, "da ma tsoffafin hanyoyin birnin Beijing kayayyakin fasaha ne. Yau da shekaru darurruka ke nan da aka gina su. Daidai kamar wani tsoho ya taba dandana wahala, wadannan tsoffafin hanyoyi ma sun tsofa, sun sha wahala, amma suna da sigarsu ta musamman har ba safai a kan iya samun irinsu ba a sauran wurare, sabo da haka ina sha'awarsu ainun."
A sakamakon ci gaba da ake samu wajen gina birnin Beijing a cikin shekarun nan da suka wuce, manyan gine-gine da ake yi kullum sai kara karuwa suke yi a cikin birnin, sa'an nan yawan tsoffafin hanyoyi sai kara raguwa yake yi. Da ganin irin wannan hali ne, yanzu gwamnatin birnin Beijing ya riga ya dauki tsaurarran matakai wajen kare wasu tsoffafin hanyoyi wadanda ke da sigogin musamman. Hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta birnin Beijing ta shirya wa masu yawon shakatawa zagayawa da su a cikin tsoffin hanyoyin birnin, ta yadda za su gana ma idanunsu da zaman rayuwa da aka yi a birnin Beijing a da. Masu yawon shakatawa za su iya zagaya tsoffin hanyoyin a kan keke mai tayoyi uku da mutane ke ja, su shiga cikin tsakar gida, wato gidan gargajiya na birnin, su sha shayi mai dadi, su saurari wasu labaru na tsohon birnin Beijing, su ji zaman rayuwar 'yan birnin.
Malam Gunter Wein wanda ya fito daga kasar Jamus ya ce, ya taba zagaya wasu tsoffin hanyoyin birnin Beijing a kan keke mai tayoyi uku da mutane ke ja, ya dudduba su sosai. Ya ce, "na taba ganin irin wannan keke a kasar Indiya, keke na da kyau kwarai, kuma ya dace da wadannan tsoffin hanyoyi, ya iya kai ka ko ina cikin hanyoyin nan, amma idan an dauki taksi, to, bai zai yi haka ba. Tsoffin hanyoyin birnin Beijing suna da nasu sigogin musamman, lale suna da kyau sosai, ina sha'awarsu fiye da manyan gine-gine da unguwoyin kasuwanni."(Halilu)
|