Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-25 21:49:15    
Babban haikalin addinin Buddah da ake kira kofar kiyaye dokoki a kasar Sin

cri

Lardin Shaanxi yana arewa maso yammacin kasar Sin. An taba kafa dauloli 12 daya bayan daya a wannan lardin a cikin sama da shekaru 3000 da suka wuce. Ya zuwa yanzu, akwai tsoffafin gine gine da tsoffafin kayayyakin al'adu da yawa wadanda suke nan samul garau a lardin. Babban haikalin addinin Buddah da ake kira kofar kiyaye dokoki yana daya daga cikinsu, kuma yau sama da shekaru 1700 ke nan da aka gina shi.

Babban haikalin addinin Buddah da ake kira kofar kiyaye dokoki yana birnin Baoji da ke a yammacin birnin Si'an, fadar gwamnatin lardin Shaanxi na kasar Sin. Nisan da ke tsakaninsa da birnin Si'an ya wuce kilomita 100. Fadinsa bai wuce kadada 7 ba. An fara gina shi ne, yayin da aka fara yadada addinin Buddah a kasar Sin yau da shekaru sama da 1700 da suka gabata. An ce, bayan rasuwar Sakyamuni wanda ya kirkiro addinin Buddah, sai aka kone gawarsa, tsoffin kayayyakin tarihin addinin Buddah da aka samu daga tokarsa, an ajiye su ne a cikin hasumiyar wurare daban daban na duniya. Daya daga cikinsu, akwai hasumiya da aka gina a babban haikalin da ake kira kofar kiyaye dokoki a kasar Sin.

A shekarar 1987, an tono tsoffafin kayayyaki masu daraja da yawansu ya wuce 2000 daga fadar da ke karkashin hasumiyar wannan babban haikalin addinin Buddah, yayin da aka rushe ta don gina wata sabuwa. Daga binciken da masanan ilmin tsoffafin kayayyaki suka yi, an gano cewa, daga cikin tsoffafin kayayyakin da aka tono daga karkashin wannan husumiya, akwai tsoffafin kayayyakin tarihin addinin Buddah da aka samu daga tokar Sakyamuni, wanda ya kirkiro addinin nan. Irin wadannan kayayyakin tarihin addinin Buddh kayayyaki ne mafi tsarki ga bangaren addinin Buddah a halin yanzu.

Malam Yao Yinliang, magajin gari na Baoji ya bayyana cewa, "ba safai a kan iya samun al'adun addinin Buddah na babban haikalin addinin Buddah mai suna kofar kiyaye dokoki a duk kasar Sin baki daya ba. A nan ne aka sami tsoffafin kayayyakin tarihin addinin Buddah na Sakyamuni, kuma an tono dimbin tsoffafin kayayyaki masu daraja na daular Tang daga karkashin kasar babban haikalin. Yanzu mu kan shirya bukukuwa a babban halikalin nan a ko wace shekara wadanda masu yawon shakatawa da yawa suka halarta. "

Tun bayan da aka yi wa wannan babban haikalin addinin Buddah kwaskwarima sosai, sai an sake bude kofarsa ga duk duniya a shekarar 1988. Ban da sabuwar hasumiyar mai tsayin mita 47 da aka gina ta hanyar yin kwikwayo yadda tsohuwar hasumiyar nan take, kuma an gina wani dakin nunin tsoffafin kayayyaki. A halin yanzu, bayan da masu yawon shakatawa suka ziyarci babban haikalin nan, su kan iya kai ziyara ga dakin nunin nan.

A kan shirya bikin yawon shakatawa irin na al'adun duniya a babban haikalin addinin Buddah mai suna kofar kiyaye dokoki a watan Afrilu na ko wace shekara. A lokacin bikin nan, a kan shirya addu'o'I da sauran harkokin addinin Buddah don neman zaman alheri, kuma a kan yi nune-nunen tsoffafin kayayyakin tarihi masu dajara kwarai. Har ma a wani sa'i, 'yan addinin Buddah su kan shirya gaggarumin bikin addu'o'i don neman tabbatar da zaman lafiya a duk duniya.

Madam Monika Westermann, 'yar yawon shakatawa wadda ta fito daga kasar Jamus tana sha'awar al'adun addinin Buddah ainun. Ta ce, ita da 'yan iyalinta sun more idanunsu sosai da irin wannan bikin yawon shakatawa da aka shirya. Ta ce, "duk harkokin da aka gudana a gun bikin yawon shakatawa na babban haikalin addinin Buddah suna da kyau kwarai, kuma ina sha'awarsu ainun." (Halilu)