Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-25 20:45:27    
Isra'ila za ta dauki matakai mafi tsanani don kai bugu ga kungiyar Hezbollah ta Lebanon, in ji Mr. Olmert

cri

Ran 25 ga wata, firaministan kasar Isra'ila Mr. Ehud Olmert ya bayyana cewa, kasasr Isra'ila za ta ci gaba da kai farmaki ga dakarun kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon, za ta kuma dauki matakai masu tsanani kan masu rike da makamai da suke harba rokoki kan kasar Isra'ila.

Mr. Olmert ya yi wannan bayani ne kafin ya yi shawarwari da sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka madam Condoleezza Rice da ke ziyarar kasar a ran nan. Madam Rice ta bayyana cewa, bangaren kasar Amurka ya mai da hankali sosai kan rikicin akidar jin kai da rikicin da ke tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila ya haddasa, ya yi kira ga bangarorin 2 da su sa aya ga rikicin da ke tsakaninsu. Amma ya jaddada cewa, tilas ne za a warware rikicin da ke tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila cikin dogon lokaci, kuma tilas ne a tabbatar da ganin cewa, kada halin da ake ciki a yanzu ya koma baya.

A sa'i daya kuma, dakarun kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon sun ci gaba da harba rokoki zuwa ga birnin Haifa da ke arewacin kasar Isra'ila, inda mutane a kalla 30 suka ji rauni. Sojojin kasar Isra'ila da ke cikin yankin kasar Lebanon sun ci gaba da dosawa arewa, sun kuma yi musayar wuta mai tsanani da dakarun kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon.(Tasallah)