|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2006-07-25 18:13:20
|
Isra'ila za ta dauki matakai mafi tsanani don kai bugu ga kungiyar Hezbollah ta Lebanon, in ji Mr. Olmert
cri
Ran 25 ga wata, firaministan kasar Isra'ila Mr. Ehud Olmert ya bayyana cewa, kasasr Isra'ila za ta ci gaba da kai farmaki ga dakarun kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon, za ta kuma dauki matakai masu tsanani kan masu rike da makamai da suke harba rokoki kan kasar Isra'ila.
Mr. Olmert ya yi wannan bayani ne kafin ya yi shawarwari da sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka madam Condoleezza Rice da ke ziyarar kasar a ran nan. A sa'i daya kuma, dakarun kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon sun ci gaba da harba rokoki zuwa ga birnin Haifa da ke arewacin kasar Isra'ila, inda mutane a kalla 30 suka ji rauni. Sojojin kasar Isra'ila da ke cikin yankin kasar Lebanon sun ci gaba da dosawa arewa, sun kuma yi musayar wuta mai tsanani da dakarun kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon.(Tasallah)
|
|
|