Ran 24 ga wata, sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka madam Condoleezza Rice ta sauka birnin Beirut, hedkwatar kasar Lebanon, don yin ziyara a nan.
A ran nan madam Rice ta sauka Beirut ne a cikin wani jirgin sama mai saukar ungulu na soja na kasar Amurka. Lokacin da take ziyarar kasar Lebanon, za ta yi shawarwari da firaministan kasar Lebanon Mr. Fouad Siniora da sauran jami'an gwamnatin kasar Lebanon. A kan hanyarta zuwa Gabas ta Tsakiya a wannan rana, madam Rice ta bayyana cewa, abin da za a yi cikin gaggawa shi ne tabbatar da tsagaita bude wuta a tsakanin kasar Isra'ila da kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon, amma abu mai muhimmanci shi ne samar da wasu sharudda a fannin tabbatar da tsagaita bude cikin dogon lokaci.(Tasallah)
|