Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-24 16:27:50    
Nashiyar Afrika tana cin gajiyar huldar abokantaka a tsakaninta da kasar Sin

cri
A cikin shirinmu na yau za mu karanta muku wani bayani da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya taho da shi, bayan da ya kai ziyara ga Mr Saku, babban sakataren zartaswa na asusun tallafin kwararru na Afrika kuma tsohon firayim ministan kasar Mali. Bayanin yana da kanun labari cewa, nashiyar Afrika tana cin gajiyar huldar abokantaka a tsakaninta da kasar Sin.

Ran 22 ga wata a lokacin da Mr Saku ke hira da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua, ya karyatar da surutun banza da kafofin watsa labaru na kasashen Turai ta yamma suka yi na wai "kasar Sin za ta mayar da Afrika da ta zama nahiyar da ke karkashin mulkin mallakarta", sa'an nan ya nuna cewa, nahiyar Afrika tana cin gajiyar kyakkyawar huldar hadin kai irin ta abokantaka a tsakaninta da Sin.

Mr Saku ya kara da cewa, irin wannan surutun banza na kafofin watsa labaru na kasashen Turai ta yamma ba wani abu ba ne sai karya ce kurum. Babu wani bincike da ya nuna cewa, kasashen Afrika suna asara daga ma'amala da suke yi a tsakaninsu da kasar Sin. Bamban d haka suna samun amfani.

Mr Saku ya ci gaba da cewa, kafofin watsa labaru na kasashen Turai ta yamma sun zargi cewa, wai kasar Sin tana gudanar da manyan ayyuka a kasashen Afrika ne, domin fitar da 'yan kwadago masu arha zuwa kasashen Afrika. Wannan ya sa mutanen Afrika da yawa suka rasa ayyukan yi. Amma abin gaskiya shi ne, kasar Sin ta samar da ayyukan yi masu dimbin yawa ga Afrika. A 'yan shekarun baya, lokacin da gwamnatocin kasashen Afrika suke aiwatar da manyan ayyuka, a galibi dai kamfanonin kasar Sin suna samun ayyukan ta hanyar gabatar da takardar neman izni, sabo da sun kware sosai. Tun da kasar Sin ta fara zuba jari da gudanar da harkokin ciki a kasashen Afrika, tana fitar da kayayyaki masu inganci da rahusa zuwa ga kasashen Afrika.

A lokacin da Mr Saku ya yi bayani a kan huldar abokantaka da ke tsakanin kasar Sin da Afrika a fannin siyasa, sai ya ce, irin wannan kyakkyawar hulda ta ba da tabbaci ga kudurin da kungiyoyin kasa da kasa suka yi sun dace da moriyar kasashe mafi talauci. A cikin aikin gyare-gyare na Majalisar dinkin duniya, kasar Sin da kasashen Afrika suna da moriya iri daya.

Mr Saku ya ce, yawancin kasashen Afrika sun fahimci cewa, kasar Sin tana girmama mallakar kan sauran kasashe, kuma ta amince da su kula da makomarsu da manufofinsu game da tattalin arziki. A hakika dai, kasar Sin tana goyon bayan gwamnatocin kasashen Afrika sosai.

Mr Saku ya kara da cewa, bayan da kasar Mali ta sami 'yancin kai, kasar Sin ta taimaka mata wajen kafa masana'antarta ta farko. Manufar kasar Sin ita ce ba don cin gumin jama'ar kasr ba, banban da haka tana son ta taimaki kasar wahen inganta 'yancinta a fannin siyasa ta hanyar samun 'yancin kai a fannin tattalin arziki. Ban da haka kuma, kasar Sin ta taimakawa kasashen Afrika wajen horar da 'yan kwadago da kwararru da yawa domin kasashen Afrika.

A shekarar 1985, Mr Saku ya taba kawo ziyara a kasar Sin, a wannan gami ma yana fata zai sake kawo ziyararsa don ganam ma idonsa ci gaba da kasar Sin ta samu a shekarun baya. Yana kuma ganin cewa, sakamakon da kasar Sin ta samu wajen yin gyare-gyare kan tattalin arziki, da tsarin kasuwanni, da jawo kudaden jari daga kasashen waje duniya ce mai daraja sosai ga kasashen Afrika. Yanzu, yawancin kasashen Afrika suna shan wahalhalu wajen bunkasuwar harkokin tattalin arziki, idan kasar Sin da kasashen Afrika sun iya cin gajiyar sakamakon nan da kasar Sin ta samu, to, kasshen Afrika za su sami fa'ida sosai.

An kafa asusun tallafin kwararru ta kasashen Afrika ne a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe a shekarar 1991, yanzu tana da mambobinta 34 na gwamnatoci ko kungiyoyi na Afrika ko duniya. Manufar asusun nan ita ce gabatar da cikakken tsarin horar da shugabannin kasashen Afrika, da sa kaimi ga bunkasuwar gwamnato da zaman al'ummar Afrika, da kara fahimtar juna da hadin guiwa a tsakanin mambobin asusun ta hanyoyi daban daban, ta haka za a kara daga matsayin gwamnatocin kasashen waje don gudanar da harkokin mulki da samun ci gaba mai dorewa. Tun daga shekarar 2000, Mr Saku ya fara rike da mukamin babban sakataren Asusun nan, wato yanzu shi ne babban shugban asusun.(Musa)