Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-24 15:47:53    
Kabilar Elunchun

cri

Mutanen kabilar Elunchun da yawansu ya kai kusan 8200 kawai suna zama a wasu wuraren jihar Mongoliya ta gida mai cin gabashin kanta da na lardin Helongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin. Kalmar Elunchun tana da ma'anoni 2, wato, mutanen da ke kiwon bareyi ko mutane wadanda suke zama a kan tsaunuka. Mutanen kabilar Elunchun suna da yarensu, amma babu kalma. Yawancinsu suna amfani da harshen Sinanci, wasu suna amfani da harshen Mongoliya.

Yawancin mutanen kabilar Elunchun suna zama a yankunan gandun daji da ke kan tsaunin Daxing'anling da ke arewa maso gabashin kasar Sin. Tsayin yawancin yankunan da suke zama ya kai mita dari 5 zuwa dubu 1 da dari 5 daga leburin teku, wato yankunan sanyi sosai. Kafin kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, muhimmiyar sana'ar da mutanen kabilar Elunchun suke yi ita ce sana'ar yin farauta. Wasu suna sana'ar kama kifi da neman 'ya'yan itatuwa kuma da yin sana'ar hannu. Kafin a 'yantattar da mutanen kabilar Elunchun a watan Agusta na shekarar 1945, yawan mutanen kabilar ya kai dubu 1 da wani abu kawai. Bayan da aka ci nasarar yakin kin harin Japan, a karkarshin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, mutanen kabilar Elunchun sun kafa wata gwamantin kabilar Elunchun mai cin gabashin kanta a yankin arewa maso gabashin kasar Sin. Tun daga shekarar 1951 zuwa shekarar 1953, gwamnatin kasar Sin ta kebe kudude masu dimbin yawa domin gina gidaje don mutanen kabilar Elunchun. Tun wancan lokaci ne, mutanen kabilar Elunchun suka fara zama a wani wuri a kai a kai. Yanzu, yawancin yaran kabilar Elunchun sun samu izinin shiga makarantun sakandare, wasu daga cikinsu sun samu izinin shiga jami'o'in kasar Sin. A da, mutanen kabilar Elunchun ba su da likita, kuma ba su da magani, amma yanzu akwai dakunan likitoci da magunguna a yankunan kabilar Elunchun, Sakamakon haka, yawan mutanenta yana ta karuwa cikin sauri. Zaman rayuwar mutanen kabilar Elunchun ma ya samu kyautatuwa a kai.

Sannan kuma, a cikin dogon lokacin da ya wuce, mutanen kabilar Elunchun sun kago al'adunsu masu launi iri iri. Suna da adabin da ake yada su a baki da kide-kide da raye-raye da zane-zane.

Mutanen kabilar Elunchun suna cin nama, kuma suna sa tufafin fatan dabbobi. Bugu da kari kuma, bisa al'adar kabilar Elunchun, wani namiji ya iya auren mace daya. Kuma suna bin addininsu na Sa'man, wato suna girmama abubuwan halittu da kakani-kakaninsu da dodon rana da dodon wata da dodannin sauran taurari. (Sanusi Chen)