Wakilin Rediyon kasar Sin ya aiko mana labari cewa , a ran 23 ga watan nan , Ehud Olmert , firayin ministan kasar Isra'ila ya bayyana cewa , gwamnatinsa a shirye take za a kafa wata rundunar sojojin kasashen Kungiyar Turai a kudancin yankin kasar Lebanon .
A wannan rana Mr. Olmert ya gana da Frank Steinmeier , ministan harkokin waje na kasar Jamus , inda ya ce , wannan rundunar sojojin kasashen duniya ya kamata ta girke a iyakar tsakanin kasar Isra'ila da Lebanon , kuma dole ne ta iya mallake hanyar mai sada Kasar Syria da Lebanon .
A wannan rana , Josh Bolten , Direktan Ofishin Fadar gwamnatin kasar Amurka ya bayyana cewa , kasarsa tana goyon bayan irin wannan rundunar sojojin , amma sojojin kasar Amurka ba za su shiga ciki ba .
Bisa labarin daban da aka bayar , an ce , Nabih Barri , shugaban Majalisar kasar Lebanon ya ce , jam'iyyar Hezbollah tana goyon bayan kudurin gwamnatin kasar Lebanon. (Ado)
|