Ran 23 ga wata, ministan tsaron kasar Isra'ila Mr. Amir Peretz ya bayyana cewa, kasar Isra'ila tana goyon bayan girke sojojin kiyaye zaman lafiya na duniya a kudancin kasar Lebanon, don warware rikicin da ke tsakaninta da kasar Lebanon a yanzu. A wannan rana kuma, shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Mr. Nabih Berri ya fayyace cewa, kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta riga ta yarda da gwamnatin kasar Lebanon da ta dauki nauyin yin musayar mutanen da aka yi garkuwa da su da kasar Isra'ila a madadinta, wannan ne karo na farko da kungiyar Hezbollah ta yarda da gwamnatin kasar Lebanon da ta dauki nauyin yin musayar mutanen da aka yi garkuwa da su a madadinta.
Bayan da ya gana da ministan harkokin waje na kasar Jamus Mr. Frank-Walter Steinmeier da ke ziyarar kasar Isra'ila a ran nan, Mr. Peretz ya bayyana cewa, saboda yanzu sojojin gwamnatin kasar Lebanon ba su iya sarrafa kudancin kasar Lebanon ba, shi ya sa kasar Isra'ila tana goyon bayan girke sojojin kiyaye zaman lafiya na duniya a wannan yanki.
A ran nan kuma, shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Mr. Nabih Berri ya bayyana a birnin Beirut cewa, kungiyar Hezbollah ta riga ta amince da gwamnatin kasar Lebanon da ta mayar da 'yan kasar Lebanon da kasar Isra'ila ta yi garkuwa da su ta hanyar yin amfani da sojoji 2 na kasar Isra'ila da kungiyar Hezbollah ta yi garkuwa da su. (Tasallah)
|