A ran 22 ga wata, wasu muhimman kungiyoyin dakaru na Palesdinu da ke zirin Gaza sun bayyana cewa, sun amince da daina harbi rokoki ga kasar Isra'ila daga ran nan da tsakar dare.
Bisa labarin da muka samu, an ce, a ran nan, shugaban hukumar al'ummar Palesdinu Mahmoud Abbas da firayim ministan gwamnatin Palesdinu mai cin gashin kai Ismail Haniyeh sun kira taron da rukunoni daban daban suka halarta a zirin Gaza, inda suka yi tattaunawa kan yadda ya kamata a sa aya ga matsalar da matakan soja da sojojin Isra'ila suka dauka a zirin Gaza suka haddasa.
Wasu muhimman kungiyoyin dakaru na Palesdinu ciki har da kungiyar Hamas da kungiyar Jihad sun bayyana bayan taron, cewa sun amince da tsagaita bude wutar yaki da kuma daina harbi rokoki ga kasar Isra'ila.(Kande Gao)
|