Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-23 17:59:35    
Sojojin kasa na kasar Isra'ila sun kutsa kai cikin kudancin kasar Lebanon

cri
A ran 22 ga wata ne aka shiga rana ta 11 na yin hargitsi a tsakanin Isra'ila da dakarun kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon. Sojojin kasar Isra'ila sun ci gaba da jefa boma-bomai a kudancin kasar Lebanon, da kuma kai farmaki ga wasu muhimman tashoshin sadarwa da na harbar siginar talibijin.

A ran nan, sojojin kasa na kasar Isra'ila sun sake wuce bakin iyakar da ke tsakanin kasashen Isra'ila da Lebanon domin kai wa dakarun kungiyar Hezbollah ta Lebanon farmaki. Sojojin kasar Isra'ila sun bayyana cewa, sojojin kasa na kasar sun riga sun sarrafa kauyen Maroun al-Ras da ke kudancin kasar Lebanon, kuma an ce wai kungiyar Hezbollah ta Lebanon ta harbi makamai masu linzami ga arewancin kasar Isra'ila a cikin kauyen. Bisa labarin dumi dumi da muka samu, an ce, a ran 23 ga wata, kakakin sojoji na wucin gadi na MDD da ke kasar Lebanon Milos Strugar ya tabbatar da cewa, sojojin kasa na kasar Isra'ila sun riga sun mamaye kauyen Marun al-Ras, muhimmin kauye ne da ke kudancin kasar Lebanon.

A ran nan kuma, firayin ministan kasar Lebanon Fouad Siniora ya fayyace cewa, yanzu gwamnatin kasar suna yin tattaunawa tare da kungiyar Hezbollah domin lallashe ta kan amincewa da tsagaita bude wutar yaki tsakaninta da sojojin Isra'ila.

A waje daya kuma, kasar Iran ta bayyana cewa, Iran ba za ta sa hannu a cikin rikicin da ke tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila ta hanyar sojoji ba, amma za ta ci gaba da nuna goyon baya ga Lebanon a fannonin siyasa da diplomasiyya. Kuma kasashen Jordan da Faransa sun sake yin kira ga kasashen Lebanon da Isra'ila da su tsagaita bude wutar yaki tsakaninsu daga dukkan fannoni nan da nan, kuma sun nuna cewa, ba za a iya hana tsanantar halin da ake ciki yanzu ba sai a tsagaita bude wutar yaki. (Kande Gao)