A ran 21 ga wata ne aka shiga rana ta 10 na yin hargitsi a tsakanin Isra'ila da dakarun kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon. Akwai alamar cewa, mai yiwuwa ne, sojojin kasar Isra'ila za su kai mummunan hare-hare a kan kasar Lebanon ta hanyar kasa.
A wannan rana, sojojin Isra'ila sun kara tattarawar tankoki da sojojin kasa masu dimbin yawa a wurare da ke bakin iyakar kasa tsakanin kasashen Isra'ila da Lebanon, kuma sun yi shelar daukar sojojin wucin gadi da yawansu ya kai 5000. Ka zalika jiragen sama na rundunar sojojin Isra'ila sun barbaza takardun farfaganda a kudancin kasar Lebanon, inda suka nemi mazaunan wuri da su yi kaura daga wurinsu nan da nan. Dan Halutz, babban hasfan hafsoshin rundunar sojojin kasar Isra'ila ya bayyana a wannan rana cewa, mai yiwuwa ne, sojojin Isra'ila za su kai farmaki a kan wasu wuraren kudancin kasar Lebanon daga kasa, don murkushe dakarun kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon wadanda ke kai barzana ga zaman lafiyar Isra'ila.
Amma kafofin watsa labaru na Isra'ila sun bayar da labarun cewa, nan da 'yan kwanaki masu zuwa, sojojin kasar Isra'ila za su kara kutsa kansu a wurare da yawa na kasar Lebanon don gwabza fada.
Bisa halin da ake ciki dangane da kara tsananta yaki da sojojin Isra'ila ke yi, Lahoud, shugaban kasar Lebanon ya bayyana a ran 21 ga wata cewa, idan sojojin Isra'ila sun kutsa kansu cikin yankin kasar Lebanon, to, sojojin gwamnatin kasar za su shiga yaki. (Halilu)
|