Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-22 17:34:43    
Kwamitin sulhu na MDD ya kira babbar muhawarra kan batun gabas ta tsakiya

cri
A ran 21 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya kira babbar muhawarra ta yini daya kan batun gabas ta tsakiya, inda wakilan kasashe fiye da 40 sun yi jabawai bi da bi. Yawancin wakilan kasashen da ke cikinsu sun yi kira ga bangarori daban daban na shiyyar gabas tsakiya da su dauki matakai don tsagaita bude wutar yaki. Amma wakilan kasashen Isra'ila da Amurka sun jaddada cewa, idan ana so a tabbatar da samun zaman lafiya a gabas ta tsakiya cikin dogon lokaci, to dole ne a kwance damarar kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon kwata-kwata.

A gun taron da aka yi a ran nan, wakilan kasashen Sin da Rasha da Birtaniya da Faransa da dai sauran kasashe sun yi kira ga bangarori daban daban na shiyyar gabas ta tsakiya da su yi hakuri domin samar da sharadda ga tsagaita bude wutar yaki nan da nan. Ban da wannan kuma kasashen suna fatan kwamitin sulhu zai mayar da martani tun da wuri kan hana matsalar da ke faruwa a gabas ta tsakiya, ta yadda zai dauki nauyin musamman a kan wuyansa wajen kiyaye zaman lafiya da tsaron kai na duniya.

Zaunannen wakilin kasar Lebanon da ke MDD Nouhad Mahmoud ya bayyana cewa, dalilin da ya sa aka ta da rikici a gabas ta tsakiya shi ne sabo da bangaren da abin ya shafa ya kyale dokokin duniya da kuma kin bin kudurin da abin ya shafa da MDD ta tsai da. Haka kuma halin da shiyyar gabas ta tsakiya ke ciki yanzu ya bukaci tsagaita bude wutar yaki nan da nan daga dukkan fannoni da kuma warware matsalar ta hanyar zaman lafiya da diplomasiyya.

Amma zaunannen wakilin kasar Isra'ila da ke MDD Dan Gillerman ya ce, idan ana so a tabbatar da samun zaman lafiya cikin dogon lokaci a shiyyar, to wani mataki da ke gaban kome shi ne kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta saki sojojin Isra'ila da ta kama da kuma kwance damararta, kuma gwamnatin kasar Lebanon za ta gudanar da dukkan ikon mulkin kasar.

Haka kuma John Bolton, zaunannen wakilin kasar Amurka da ke MDD ya sake jaddada cewa, muddin a kwance damarar kungiyar Hezbollah ta Lebanon, sai kasar Isral'ila za ta iya gudun farmakin ta'addanci da aka kai mata, kuma 'yan kasar Lebanon za su iya fid da kansu daga hannun kungiyar Hezbollah, ta haka za a iya tabbatar da samun zaman lafiya cikin dogon lokaci a shiyyar gabas ta tsakiya.(Kande Gao)