A ran 21 ga wata, a gun taron muhawarra da aka yi a kwamitin sulhu na MDD kan batun gabas ta tsakiya, Liu Zhenmin, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD ya yi kira ga kwamitin sulhu da ya dauki matakai masu amfani tun da wuri domin sassauta matsalar da ke tsakanin kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon da kasar Isra'ila.
Haka kuma Liu Zhenmin ya bayyana cewa, bisa kundin tsarin MDD, ya kamata kwamitin sulhu ya dauki nauyi mafi muhimman a kan wuyansa a fannin kiyaye zaman lafiya da tsaron kai na duk duniya. Tun da aka ta da rikicin da ke tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila, kasashen duniya da mutanen shiyyar gabas ta tsakiya suna mai da hankali sosai kan abubuwan da kwamitin sulhu ke yi. Bangaren Sin yana fatan kwamtin sulhu ba zai kaucewa burinsu ba, da kuma mayar da martani kan batun da wuri ta hanyar bayyana ra'ayinsa mai muhimmanci.
A waje daya kuma, fadar shugaban kasar Faransa ta bayar da sanarwa a ran 21 ga wata, cewa shugaban kasar Faransa Chirac ya riga ya bukaci kungiyar gamayyar Turai da ta ba da umurni kan cewa, a madadin kungiyar, Javier Solana, babban wakilin kungiyar mai kula da harkokin diplomasiyya da manufofin tsaron kai zai dukufa kan sassauta halin da kasar Lebanon ke ciki yanzu tare da MDD, ta yadda za su sa kaimi ga bangarori biyu na Lebanon da Isra'ila da su rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar tsagaita budu wutar yaki ta dogon lokaci.(Kande Gao)
|