Jama'a masu karatu, yanzu ga shirinmu na yau na Bunkasuwar kasar Sin. A cikin shirinmu na yau za mu bayyana muku yadda ake neman bunkasuwar tattalin arziki tare da kiyaye yanayin sauti a sabuwar unguwar Binhai ta birnin Tianjin na kasar Sin.
A gun taron shekara-shekaraa na majalisar dokokin kasar Sin da aka yi a watan Maris na wannan shekara, yadda za a raya sabuwar unguwar Binhai ta birnin Tianjin da ke bakin teku na kasar Sin ya zama daya daga cikin muhimman ayyukan neman bunkasuwa da gwamnatin kasar Sin za ta yi yunkurin cimmawa a cikin shekaru 5 masu zuwa. Bisa shirin da aka tsara, wannan sabuwar unguwar Binhai ta birnin Tianjin za ta zama wani sashen kira na zamani da wata cibiyar zirga-zirgar jiragen sama da cibiyar sufurin kayayyaki kuma da unguwar da ke sada abuta a tsakanin dan Adam da yanayin sauti.
Lokacin da ake cikin shekaru 90 na karnin da ya gabata, a bayyane ne gwamnatin birnin Tianjin ta bayar da shirin raya sabuwar unguwar Binhai. Yau da shekaru 10 da suka wuce, an fara ayyukan raya shiyyar raya tattalin arziki da fasahar zamani ta Tianjin, a takaice dai ana kiransa Teda. Teda muhimmin sashe ne na sabuwar unguwar Binhai. Ya zuwa karshen shekara ta 2005, yawan masana'antun jarin waje da aka kafa a shiyyar Teda ya riga ya wuce dubu 4, jimlar jarin waje da aka zuba a shiyyar ta riga ta kai dalar Amurka fiye da biliyan 29.
A shekarar 1994, kamfanin Motorola ya kafa wata masana'antar kera wayoyin salula na GSM. Mr. Yang Boning wanda ke kula da harkokin yada labaru da harkokin jama'a a sashen Motorola da ke kasar Sin ya bayyana cewa, "Kasar Sin tana da muhimmanci sosai ga kamfanin Motorola a duk fadin duniya. Kasuwar kasar Sin ta fi sauran na kasashen duniya girma. Sannan kuma, wayoyin salula na GSM da aka kera a nan kasar Sin ba ma kawai suna biyan bukatun kasuwar kasar Sin ba, har ma ana fitar da su zuwa sauran kasashen duniya. Bugu da kari kuma, ba ma kawai ana kera wayoyin salula na GSM na Motorola a nan kasar Sin ba, ana har kuma ana nazarin fasahohin zamani a sashen Motorola da ke nan shiyyar Teda ta birnin Tianjin. Mun yi nazari kan ayyuka da yawa ba domin kasuwar kasar Sin kawai ba, amma domin kasuwannin sauran kasashen duniya."
Lokacin da ake raya shiyyar Teda, jami'ai wadanda suke tsara shirin raya sabuwar unguwar Binhai sun fara yin nazari kan yadda za a kara neman bunkasuwa bisa sharadin tashar ruwa ta Tianjin.
Fadin tashar ruwa ta Tianjin da ke kunshe da filin ruwa da filin kasa ya kai kusan murabba'in kilomita dari 2. Jirgin ruwa da ke iya daukar kayayyaki ton dubu 150 zai iya shiga tashar a ko da yaushe kuma a kowace rana. Yawan kayayyakin da ake wucewa da su tashar ruwa ta Tianjin ya kai fiye da ton miliyan dari 2.
Lokacin da ake mai da hankali wajen neman bunkasuwar tattalin arzikin sabuwar unguwa ta Binhai ta birnin Tianjin, gwamnatin sabuwar unguwa ta Binhai tana kuma mai da hankali kan yadda za a nemi bunkasuwar zaman al'umma tare da kiyaye muhallin da ake ciki. Yanzu fadamar da fadinta ya kai murabba'in kilomita fiye da dari 5 ta riga ta samu kiyayewa. Fadin itatuwa da ciyayi ya kai kashi 35 daga cikin kashi dari na duk fadin unguwar. Ingancin ruwa da aka samu daga ruwa maras tsabta ya riga ya wuce ma'aunin ruwan sha.
Lokacin da wakilinmu yake yawo a sashen kamfanin Sino-Chem da ke birnin Tianjin, ya ga bareyi da dawisu suna yawo suna wasa a kamfanin. Bugu da kari kuma, an dasa itatuwa da ciyayi da furanni iri iri a kamfanin. Mr. Zheng Wanjun wanda ke kula da sashen kamfanin Sino-Chem da ke birnin Tianjin ya bayyana cewa, "Mun dasa itatuwa da ciyayi a cikin kamfanin domin kyautata ingancin iska yayin da muke sarrafa kayayyaki masu kazamtarwa. Alal misali, kafin mu fitar da ruwa mai kazamtarwa, masana'antar da muke ciki ta kan sarrafa shi da wuri, daga baya, ruwa ya shiga masana'antar sarrafa ruwa mai kazamtarwa ta babban kamfanin. Bayan da ingancin ruwa ya dace da ma'aunin kasar Sin, sai mu fitar da shi zuwa kogi da teku."
Domin tattalin arziki da muhalli suna samun cigaba da kyautatuwa tare, mazauna wadanda suke da zama a sabuwar unguwar Binhai suna jin dadin zaman rayuwa da aikinsu. Madam Florenee Cherry wadda ta zo daga kasar Amurka yanzu tana aiki a sabuwar unguwar Binhai ta birnin Tianjin, tana jin mamaki da ganin aikin kiyaye muhalli da hukumar sabuwar unguwar Binhai take yi. Madam Cherry ta ce, "Sun dade suna kwashe takardu da kayayyakin karfe da na leda iri iri kamar yadda mu Amurkawa muke yi. A nan ba a yi watsi da takardu da kayayyakin karfe da aka yi amfani da su ba, za a sake yin amfani da su. Sabo da haka, za a iya kiyaye muhallin da muke ciki. Wannan yana da muhimmanci sosai wajen kiyaye duniyarmu."(Sanusi Chen)
|