Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-21 11:59:21    
Ana yin rikici a tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila har kwanaki 9

cri

Ran 20 ga wata, wato rana ta 9 ce da ake ci gaba da bata kashi tsakanin kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon, da kasar Isra'ila, sojojin Isra'ila sun ci gaba da kai harin soja ga shiyyar da ke kudancin Beirut, babban birnin kasar Lebanon, da kuma shiyoyyin da ke kudancin kasar.

A ranar kashegari, sojojin kasar Isra'ila suna ci gaba da shiga shiyyar da ke kudancin kasar Lebanon, kuma suna yin dauki ba dadi da dakarun kungiyar Hezbollah. Bisa labarin da muka samu daga jaridar "Haaretz" an ce, sojojin Isra'ila 2 sun mutu a sakamakon rikicin. Wani jami'in sojoji na Isra'ila ya ce, sojojin Isra'ila za su ci gaba da dauki matakin soja a kasar Lebanon, har zuwa lokacin da kasar Isra'ila ta samu tabbaci wajen kwanciyar hankali.

A wannan rana, Fawzi Salloukh, ministan harkokin waje na kasar Lebanon ya yi wani jawabi gidan talibijin, inda ya bukaci kwamitin sulhu na M.D.D. da ya yi la'akari da sauri kan karar da kasar Lebanon ya yi wa Isra'ila, kuma ya bukaci kasar Isra'ila da ta tsagaita bude wuta nan da nan. Ya jadadda cewa, gwamnatin kasar Lebanon da kungiyar Hezbollah ba za su karbi ko wane sharuda ba kafin kasar Isra'ila ta tsagaita bude wuta.

A wannan rana kuma, Kofi Annan, babban sakataren M.D.D. ya ce, bisa shawarar da tarrayar shiga tsakani M.D.D. mai kunshe da mutane 3 da ke kula da ayyukan warware hargitsin Gabas ta tsakiya ta bayar, idan ana fatan tabbatar da tsagaita bude wuta, tilas ne a saki sojojin Isra'ila, da kara sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa Lebanon, da kuma girmama wa bakin iyakar kasa na "Shudin hanya". A wannan rana kuma, ministan harkokin waje na kasar Rasha ya bayar da wata sanarwa, inda ya bukaci bangarorin Lebanon da Isra'ila da nan da nan su tsagaita bude wuta, domin tabbatar da kare lafiyar farar hula ta yadda za su iya janye jiki daga shiyyar da ake yin rikici a ciki, da kuma samar dama wajen warware matsala ta hanyar yin shawarwarin siyasa. A wannan rana kuma, Mr. Bush, shugaban kasar Amurka ya zanta da firayin ministan kasar Turky ta waya, domin tattauna matsalar rikicin. (Bilkisu)