Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-20 15:57:29    
(Sabunta) Kasashen duniya suna ci gaba da yin kokari ta hanyar siyasa, domin warware rikicin da ke tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila

cri

Ran 19 ga wata, an ci gaba da rikici a tsakanin kasar Isra'ila, da dakarun kungiyar Hezbollah na kasar Lebanon. A sa'i daya kuma, kasashen duniya suna ci gaba da yin kokarin harkokin siyasa, domin warware rikicin.

Ran 19 ga wata a Madrid, tawaya shiga tsakani ta M.D.D. da ke kunshe da mutane 3, wadanda ke kula da rikicin da ake yi a tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila ta karfafa yin kira ga bangarorin biyu da su amince da yarjejeniya kan iyuwar girke sojojin kasashe da dama a shiyyar da ake rikicin, kuma ta yi kira ga kasashe daban daban da su aika da sojoji zuwa shiyyar. Bisa labarin da muka samu an ce, ran 20 ga wata da safe, a gun taron kwamitin sulhu, babban sakataren M.D.D. Kofi Annan ya yi hakikanin bayani kan aika da sojojin duniya zuwa kasar Lebanon.

Ran 19 ga wata, Mr. Li Zhaoxing, ministan harkokin waje na kasar Sin ya zanta da Saad Hariri, shugaban kungiyar Al Mustaqbal ta waya, bisa gayattar da aka yi masa. Ya bayyana cewa, bangaren Sin ya yi kira ga bangarorin biyu da ke cikin rikici da nan da nan su daina dauka matakin soja, domin hana kara tabarbarewar halin da ake ciki.

Ya zuwa yanzu, yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sakamakon jefa boma bomai da kasar Isra'ila ta yi wa Lebanon ya kai 237, yayin da mutane fiye da 800 suka jin rauni. Kungiyar Hezbollah ta Lebanon ta kuma kai hari da makaman roka 750 a kalla kan Isra'ila. Sakamakon haka, mutanen Isra'ila 25 sun mutu. Bisa kara tabarbarewar halin rikicin soja da ake ciki tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila, kasashe daban daban suna kwashe mutanensu daga kasar Lebanon daya bayan daya. (Bilkisu)