Ran 19 ga wata, ana ci gaba da rikici a tsakanin kasar Isra'ila, da jam'iyyar Hezbollah, dakarun kungiyar Hezbollah na kasar Lebanon. A sa'i daya kuma, kasashen duniya suna ci gaba da yin kokarin harkokin siyasa, domin warware rikicin.
Ran 19 ga wata, Mr. Li Zhaoxing, ministan harkokin waje na kasar Sin ya zanta da Saad Hariri, shugaban kungiyar Al Mustaqbal ta waya, bisa gayattar da aka yi masa, kuma sun yi musaya ra'ayoyinsu kan halin da Gabas ta tsakiya ke ciki a yanzu. Ya bayyana cewa, bangaren Sin ya yi kira ga bangarorin biyu da ke cikin rikici da nan da nan su daina dauka matakin soja, domin hana kara tabarbarewar halin da ake ciki.
A wannan rana, Javier Solana, babban wakilin kungiyar tarrayar kasashen Turai mai kula da manufar harkokin waje da kwanciyar hankali ya bayyana cewa, ya kamata kasar Isra'ila ta yi hakuri kan matakin soja da kungiyar Hezbollah ta ke yi, domin gudun yi wa farar hula illa.
A wannan rana, Mr. Chirac, shugaban kasar Faransa ya kara yin kira ga kasar Lebanon da ta tsagaita bude wuta, a sa'i daya kuma kafa wata "hanyar jin kai" a kasar Lebanon, haka kuma za a iya mayar da jama'a lami lafiya. A wannan rana kuma, kungiyar agaji ta red cross ta duniya ta yi kira ga bangarorin Lebanon da Isra'ila da su bi kaidar jin kai ta duniya. (Bilkisu)
|