Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-19 19:58:11    
Wani abu musannan na al'adun kasar Sin

cri

Wang Fuli ita ce wata shaharariyar 'yar wasan sinima ta kasar Sin. Ta sami kwarewa a matakai da yawa na tarihin raya sinimar kasar Sin, ta fito a wasannin sinima da yawa tare da sifoffinta da ke da bayyanuwar halayen musamman sosai.

A shekarar da muke ciki, Malama Wang Fuli ta cika shekaru 57 da hauhuwa, amma tamkar ba ta kai shekarun nan da haihuwa ba,domin kuwa har yanzu ta kasance cikin kuzari, mata ce mai nuna tausayi kuma mai sa himma wajen ba da taimako ga sauran mutane kuma mai saki jiki wajen yin ma'amala da mutane, kullum tana kasancewa cikin himma da kwazo wajen yin zaman rayuwa da yin sha'anin wasannin fasaha. Mahaifinta shi ne wani mashahurin mai kishin wasannin kwaikwayon Opera, wato wasan "Beijing Opera", shi ya sa tun lokacin da take karama har zuwa yanzu, tana da sha'awa sosai ga wasan "Beijing Opera". Lokacin da ta cika shekaru 11 da haihuwa, ta je karatun ilmin wasan "Beijing Opera" a makarantar koyar da ilmin wasan " Beijing Opera". Ta sami ci gaba da sauri bisa sanadiyar nuna hazikanci da kyawawan sifofi a cikin wasannin da ta yi . Bayan da ta kammala karatun, sai ta sami aikin yi a wata kungiyar nuna wasan "Beijing Opera" ta lardin Jiansu na kasar Sin, wato daga nan ne ta zama 'yar wasa ta kungiyar.

Kodayake tun lokacin da take karama tana da sha'awa sosai ga nuna wasannin sinima, amma ba ta yi tsammanin cewar ta iya zama 'yar wasan sinima ba. A shekaru 70 na karnin da ya shige, wata ma'aikatar hada finafinan sinima ta birnin Changchun na kasar Sin ta yi shirin hada wani fim na sinima mai suna " wata hanya mai walkiya", shi ya sa ma'aikatar ta dukufa wajen neman wata babbar 'yar wasan sinimar a duk fadin kasar Sin, a karshe dai ta zabi malama Wang Fuli don ta zama 'yar wasan sinimar. A wancan zamani, a kasar Sin , finafinan sinimar da aka dauka kadan ne ba da yawa ba, shi ya sa aka zabi malama Wang Fuli don ta zama babbar 'yar wasan sinimar ba abu mai sauki ba ne gare ta. A cikin sinimar, malama Wang Fuli ta sami nasara sosai wajen nuna fasahar wasanni, da sauri kusan kowane iyali na kasar Sin ya san ta. Ta ce, a kan dakalin nuna wasan "Beijing Opera", ana bin tsarin wasan nan sosai da sosai, amma a cikin sinima, a kan bayyana yadda ake yin zaman rayuwa, da farko, ban saba da aikin nan ba, amma bayan da aka gaya mini yadda nake nuna wasanni, nan da nan na saba da aikin nuna wasannin sinima.

Bayan wasu shekarun da suka wuce, Malama Wang Fuli ta zama 'yar wasan da ke da sifar wata bakauya a cikin sinima mai suna "Niu Baisui namu na kanmu", 'Yan kallo na kasar Sin sun amince da wannan sifar bakauya da ta nuna, shi ya sa ta sami lambar yabo sosai.

A cikin sinimar da aka dauka bisa jagorancin babban mutum kuma mashahurin mai daukar sinima na kasar Sin Xie Jin, wato a cikin sinimar da ake kira "Abubuwa masu mamaki da suka faru a tsaunukan Tianyunshan", akwai wani wasan da aka yi ta hanyar duka wato fada a tsakanin 'yan wasan sinimar, ashe, fadar a tsakaninsu na gaskiya ne, malama Wang Fuli ta waiwaya cewa, a karo na farko, na yi hakuri sosai, amma ban yi tsammani cewa, mai jagorancin wasan ya ce , abin da na yi bai biya bukatun da aka yi ba, dole ne a sake yin fadar, wato babban dan wasan sinimar wato mijina cikin sinimar zai sake mari na, kai marin nan da ya yi da karfi sosai, har ban iya tsayawa sosai ba, amma ba abin da na yi, sai ci gaba da hakuri kawai.

Malama Wang Fuli ta taba daukar sinima da yawa tare da halayenta na musamman na nuna wasannin sinima. Domin daukar sinima, malama Wang Fuli ta soma shan taba, ta gaya wa manema labaru cewa,da farko, ban saba da shan taba ba, amma a kai a kai ne na saba da shan taba, amma wannan ba ya da kyau ga 'yar wasa, sai na ki shan taba, a karshe dai na dakatar da shan taba bayan da na sha wahaloli da yawa. Ta ce wani lokaci ta iya waiwayon ayyukan da ta yi a da domin daukar sinima, yanzu tana jin dadin zaman rayuwarta sosai.(Halima)