Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-19 19:58:07    
Ana gaggauta ayyukan kawar da hadari da na ba da agaji a wuraren dake fama da bala'in ambaliyar ruwa a kudancin kasar Sin

cri

An yi ruwan sama mai yawan gske kamar da bakin kwarya a wassu wuraren dake kudancin kasar Sin sakamakon mummunan tasirin mahaukaciyar guguwar Bilis mai lamba 4 a wannan shekara, inda mutane 200 suka rasa rayukansu kuma mutane fiye da miliyan 25 suka sha masifa daga bala'in. Sassan da abun ya shafa na kasar Sin da kuma gwamnatocin lardunan dake fama da bala'in sun rigaya sun fito da jerin shirye-shiryen daidaita matsaloli na gaggawa da kuma gaggauta ayyukan kawar da hadari da na ba da agaji ga jama'ar dake fama da bala'in.

Jama'a masu sauraro, mun gaya muku, cewa kawo yanzu, kwanaki da dama ke nan da mahaukaciyar guguwar Bilis ta bugi wuraren dake kudancin kasar Sin, inda ruwan koguna na lardun Hunan ,da lardin Guangdong da kuma lardin Fujian da dai sauran larduna ya cika tare da aukuwar ambaliyar ruwa kan tsaunuka ; Ga ruwa ya cinye gonakai, kuma hanyoyin mota sun katse. Yin haka, ya janyo mugun tasiri ga zaman rayuwar jama'a na wuraren dake fama da bala'in. Madam Jiao Meiyan, shugabar tashar yanayin sama ta kasar Sin ta bayyana,cewa : ' Lallai mahaukaciyar guguwar Bilis da aka gamu da ita a wannan gami ta janyo mana mummunan tasiri. Daidai kamar yadda muka yi zaton, cewa an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya da yawansa ya wuce mm. 100 a wuraren dake da nisan kilomita 1,000 na kudancin kasarmu bayan raguwar karfin iska mai sassauci na sararin samaniya'.

Yanzu, ana gaggauta ayyukan kawar da hadari da na ba da agaji a wuraren da bala'in ya shafa. Bayan aukuwar bala'in ambaliyar ruwan, muhimman hanyoyin dogo da na mota wadanda suka hada Beijing da Guangzhou da kuma Beijing da Zhuhai sun katse kuma motoci da yawa sun fada cikin ruwa. Mr. Yuan Wenbiao, daraktan ofishin sarrafe-sarrafen harkokin zirga-zirgar jiragen kasa na Guangzhou ya fadi, cewa: ' Da yake ruwan sama ya mamaye hanyar dogo, shi ya sa muka tsaida kudurin kauratar da fasinjoji daga jirgin kasa zuwa wani matsuguni lami-lafiya'.

Domin kara gudanar da ayyukan kawar da hadari da na ba da agaji da kyau, sassan da abun ya shafa na kasar Sin sun ware kudin kasar Sin wato Renminbi Yuan miliyan 65 musamman domin tallafa wa jama'ar dake fama da bala'in. Ban da wannan kuma, ma'aikatar kula da harkokin jama'a ,da ma'aikatar tsare ruwa ,da ma'aikatar sufuri da kuma babbar hukumar yanayin sama na kasar Sin sun aika da wata hadaddiyar kungiya zuwa wuraren da bala'in ya shafa domin ba da jagoranci ga ayyukan riga-kafin bala'in ambaliyar ruwa da na ba da agaji.

An bayyana, cewa yanzu guguwar Bilis na kaura zuwa kudu maso yammacin yankin kasar Sin. Hakan ya kawo ruwan sama mai yawa a jihar Guangxi ta kabilar Zhuan mai cin gashi kanta da kuma lardin Yunnan. Mr. Tian Yitang, mataimakin daraktan ofishin babbar hedkwatar ba da jagoranci ga yaki da bala'in ambaliyar ruwa da fari ta kasar Sin ya furta, cewa: ' Tilas ne a mai da hankali sosai kan yiwuwar aukuwar bala'in ambaliyar ruwa kan tsaunuka da na zaizayewar kasa a wadannan wurare'.

Yanzu, an riga an yi jigilar barguna, da gidajen sauro, da tantuna da kuma tufafi da dai sauran kayayyakin agaji da yawansu ya wuce 6,000 zuwa wadannan wurare domin tabbatar da samun zaman jin dadi ga jama'ar wuraren da bala'in ya shafa. (Sani Wang )