Kwanan nan, tsohon mai sauraronmu daga birnin Abuja na tarayyar Nijeriya, Salisu Dawanau ya rubuto mana cewa, shafinku na 'internet' da kuma sabon mujallarku na 'Zumunci' wasu kafofi ne masu inganci wajen dada samun labarai dangane da kasar Sin da kuma jama'ar kasar Sin baki daya. Yau, wani abokina da na aika masa mujallarku ya tabbatar mini cewar, ya ji dadin mujallar da kuma abin da ta kunsa. Haka kuma abokin nawa yana jin dadin duba shafin naku mai kayatarwa da kuma inganci. To, mun gode, malam Dawanau, gaskiya wannan wasikarka ta karfafa mana gwiwa. Idan kun ji dadin abubuwan da muka kawo muku, to, mu ma mun ji dadin aikinmu. Nan gaba, za mu kara kokarinmu, don kara kawo muku shirye-shirye da shafin internet da mujalloli da dai sauran kafofi masu kyau.
Bayan haka, mai sauraronmu daga birnin Kano na Nijeriya, Musa Tijjani ya rubuto mana cewa, yana jin dadin shirye-shiryenmu, musamman al'adun kasar Sin. To, malam Musa, mun gode. Muna fatan za ka kara sa kulawa a kan shirye-shiryenmu.
Bayan haka, mai sauraronmu daga birnin Zaria na jihar Kaduna na tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, mun shiga gasar kacici-kacici da kuka yi a shekarar bara, amma har yanzu ba mu ji sakamakon wadanda suka sami nasara ba, da fatan za ku sanar da mu wadanda suka sami nasara. Amma a hakika, tun tuni mun sanar da masu sauraronmu a kan wadanda suka sami nasara a cikin wannan gasar kacici kacici da muka shirya a shekarar bara ta wannan shirinmu na amsoshin wasikunku da kuma shafinmu na internet, amma kuma, bari mu sake sanar da ku a kan samakakon.
Daga ran 18 ga watan Satumba zuwa ran 20 ga watan Disamba na shekara ta 2005, mun shirya gasar kacici-kacici game da 'Taiwan wani tsibiri ne mai ni'ima na kasar Sin'. Daga cikin wadanda suka shiga gasar, sashen Hausa ya zabi mutum daya wanda ya sami kyautar musamman, kuma wannan mutumin da ya taki sa'a shi ne malam. Abdullahi Garba Baji daga jihar Kano ta tarayyar Nijeriya. Bisa gayyatar da muka yi masa, malam Baji ya riga ya kawo ziyara a nan kasar Sin har ma ya koma Nijeriya. Ban da wannan kuma, sashen Hausa ya zabi mutane 5 da suka sami matsayi na farko, da 8 da suka sami matsayi na biyu da kuma mutane 12 da suka sami na uku.
Wadanda suka sami matsayi na farko su ne:
1) Malam Yahaya Salisu daga jihar Nassarawa ta tarayyar Nijeriya
2) Malam Musa Buba dan Fulani daga jihar Bauchi ta kasar Nijeriya
3) Malam Auwal Muh'd Maunde daga jihar Adamawa ta kasar Nijeriya
4) Malam Ibrahim Z.Othman daga jihar Kaduna ta kasar Nijeriya
5) Malam Abdulhadi Abubakar daga jihar Gombe ta kasar Nijeriya
Wadanda suka sami matsayi na biyu su ne:
1) Malam. Shu'ai M.Koshe /Itas daga jihar Bauchi ta kasar Nijeriya
2) Shugaba Bello Abubakar Malam Gero daga jihar Sokoto ta kasar Nijeriya
3) Malam.Ladidi Rabi'u A.Usman Mailu daga jihar Jigawa ta kasar Nijeriya
4) Malam.Sani Dahiru daga jihar Palateau ta kasar Nijeriya
5) Malam.Umar Abubakar Jalingo daga jihar Nassarawa ta kasar Nijeriya
6) Malam.Ibrahim Muhammed Zaria daga jihar Abuja ta kasar Nijeriya
7) Malam.Abba Sabo daga jihar Jigawa ta kasar Nijeriya
8) Shugaba alhaji Karami daga jihar Bauchi ta kasar Nijeriya
Wadanda suka sami matsayi na uku su ne:
1) Mrs.Maryam Musa daga jihar Nassarawa ta kasar Nijeriya
2) A'isha Mammai daga jihar Katsina ta kasar Nijeriya
3) Jamilu Muh'd daga jihar Gombe ta kasar Nijeriya
4) Baba Mala Kachalla daga jihar Borno ta kasar Nijeriya
5) Fatsuma Isah daga jihar Yobe ta kasar Nijeriya
6) Lubabatu Ahmed KD daga jihar Taraba ta kasar Nijeriya
7) Ya'u Hoh'd Bakanike daga jihar Niger ta kasar Nijeriya
8) Ali Aliyu D.K. Kamba daga jihar Kebbi ta kasar Nijeriya
9) Safiya Salisu daga jihar Jigawa ta kasar Nijeriya
10) Salihu Adama daga jihar Nassarawa ta kasar Nijeriya
11) Abubakar SadiqNingi daga jihar Bauchi ta kasar Nijeriya
12) Hamid Ahmed Buhari daga jihar Adamawa ta kasar Nijeriya
Kamar yadda muka alkawarta, mun riga mun aiko da kyaututtuka ga wadanda suka sami nasara a cikin gasar. Wadanda ba su sami nasara ba kuma, kada dai ku yi faduwar gaba. Muna fatan za ku kara yin kokari, don samun nasara a gasar kacici-kacici da za mu shirya a nan gaba.(Lubabatu)
|