Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-19 16:59:59    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(13/07-19/07)

cri
Ran 11 ga wata, a gun gasar ba da babbar kyauta ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya da aka yi a birnin Lausanne, dan wasan kasar Sin Liu Xiang ya zama zakara a cikin gasar gudun ketare shinge mai tsawon mita 110 da dakika 12.88, ya kuma karya matsayin bajimta na duniya na dakika 12.91, wanda shahararren dan wasan kasar Birtaniya Colin Jackson ya samar da shi yau da shekaru 13 da suka gabata.

A gun karin gasa ta rukunin kungiyoyin duniya ta gasar cin kofin Federation ta wasan kwallon tennis ta shekarar 2006 da aka kammala a ran 16 ga wata, kungiyar wasan kwallon tennis ta mata ta kasar Sin ta lashe kungiyar wasan kwallon tennis ta kasar Jamus da ci 4 da 1, ta haka a karo na farko ne ta shiga cikin jerin kungiyoyi guda 8 masu karfi a gun gasar cin kofin Federation. Gasar cin kofin Federation, gagarumar gasa ce ta tsakanin kungiya-kungiya na mata da hadaddiyar kungiyar wasan kwallon tennis ta duniya ta kan shirya sau daya a ko wace shekara.

Ran 16 ga wata, a Amsterdam na kasar Holland, a cikin karon karshe na gasar cin kofin zakara ta mata ta shekarar 2006 da hadadiyyar kungiyar wasan kwallon hockey ta duniya ta shirya, kungiyar wasan kwallon hockey ta kasar Sin ta sha kaye daga hannun 'yan wasan kwallon hockey na kasar Jamus da ci 2 da 3, wato ta zama ta biyu. 'Yar wasan kasar Sin Fu Baorong ta zama 'yar wasa mafi nagarta a wannan gami. Gasar cin kofin zakara ta mata na daya daga cikin gagaruman gasannin wasan kwallon hockey da a kan shirya ga mata a ko wace shekara, inda kungiyoyi 6 da ke gaba a cikin jerin kasashen duniya suka kara da juna.

An bude gasar cin kofin Asiya ta wasan kwallon kafa ta mata ta shekarar 2006 a birnin Adelaide na kasar Australia a ran 16 ga wata. Kungiyoyin wasan kwallon kafa guda 6 sun shiga wannan gasa. A rana ta farko, kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Thailand ta lashe kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Myanmar da ci 2 da 1, kungiyar kasar Australia ta lashe kungiyar kasar Korea ta Kudu da 4 ba ko daya. Kungiyar kasar Sin za ta kara da kungiyar Taipei ta kasar Sin a ran 19 ga wata. Za a kammala wannan gasa a ran 30 ga watan da muke ciki.

Ran 16 ga wata, an kawo karshen gasar cin kofin duniya ta wasan lankwashe jiki ta duniya da aka yi a Shanghai na kasar Sin, 'yan wasan kasar Sin sun nuna rawar gani, sun kwashe lambobin zinare 8 da na azurfa 4 da na tagulla 2 a cikin gasanni 10, ta haka, kasar Sin ta zama ta farko a fannin samun lambobin yabo a wannan gami.(Tasallah)