Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-19 16:57:32    
Wasu kasashe sun ci gaba da yin kira ga kasashen Lebanon da Isra'ila da su tsagaita bude wuta a tsakaninsu

cri

Ganin yadda hargitsi yake kara zafi tsakanin kungiyar Hizballah ta kasar Lebanon da Isra'ila, a ran 18 ga wata, wasu kasashe sun ci gaba da yin kira ga kasashen Lebanon da Isra'ila da su tsagaita bude wuta a tsakaninsu.

Al-Baghdadi Ali-Mahmoudi, sakatare-janar na babban kwamitin jama'ar kasar Libya ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da ta dauki matakin gaggawa wajen hana kasar Isra'ila kai hare-hare kan kasar Lebanon.

Mr Hosni Mubarak, shugaban kasar Masar ya nuna cewa, matakin soja da kasar Isra'ila ke dauka a kan Lebanon ya kara tsanani, zai jefa duk yankin gabas ta tsakiya cikin hadari, jama'ar Falasdinu da ta Lebanon za su iya sadaukarwa..

Saud Al-Faisal, ministan harkokin waje na kasar Saudi Arabiyya ya nemi manyan kasashe da su sauke nauyin da ke kansu, su sassauta mumunan halin da ake ciki. Ya jaddada cewa, abin da ya fi muhimmanci a yanzu shi ne kasashen Lebanon da Isra'ila su tsagaita bude wuta a tsakaninsu. (Halilu)