Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-19 16:11:34    
Ana cin gaba da rikicin da ake yi a tsakanin Lebanon da Isra'ila, kasashen duniya suna cin gaba da kokarin diplomasiyya

cri

Ana cin gaba da rikicin da ake yi a tsakanin Lebanon da Isra'ila, wanda ya fara daga ranar 12 ga wata. Ya zuwa yanzu, Isra'ila ta jejjefa boma bomai ga wurare da yawa na Lebanon, a sakamakon haka mutane a kalla 237 sun mutu, a sa'i daya kuma, kungiyar Hezbullah ta harba rakoki a kalla dari 7 da 50 a kan Isra'ila, a sakamakon haka, mutanen Isra'ila 25 sun raya rayukansu.

A ranar 18 ga wata, firayin minstan Isra'ila Ehud Olmert ya bayyana cewa, sojojin Isra'ila za su ci gaba da kai farmaki a kan dakarun kungiyar Hezbullah, har sai kungiyar Hezbullah ta saki sojojin Isra'ila da ta kama da tabbatar da zaman lafiyar jama'ar Isra'ila.

Ko da yake haka ne, amma kasashen duniya suna cin gaba da yin kokari domin warware rikicin ta hanyar diplomasiyya, firayin ministan kasar Faransa Dominique Galouzeau De Villepin da babban wakilin kungiyar EU mai kuloa da manufofin diplomasiyya da zaman lafiya Javier Solana da kuma tawagar shiga tsakani ta MDD mai kunshe da mutane 3 da ke da nauyin samun sulhuntawa sun riga sun je birnin Beirut, babban birnin kasar Lebanon(Danladi)