Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-19 10:48:32    
Firayin minstan Isra'ila ya bayar da sharadin tsagaita bude wuta

cri

A ran 18 ga wata, ana cin gaba da rikicin da ake yi a tsakanin Lebanon da Isra'ila. A ran nan, firayin minstan Isra'ila Ehud Olmert ya bayyana cewa, sojojin Isra'ila za su ci gaba da kai farmaki a kan dakarun kungiyar Hezbullah, har sai kungiyar Hezbullah ta saki sojojin Isra'ila da ta kama da tabbatar da zaman lafiyar jama'ar Isra'ila.

Mr Olmert ya ci gaba da cewa, Isra'ila tana fatan gwamnatin Lebanon za ta girke sojojinta a kudancin Lebanon bisa kuduri mai lamba 1559 na kwamitin sulhu na MDD, kuma su kwance damarar dakarun kungiyar Hezbullah. Ya ce, Isra'ila ba za ta yi adawa da warware rikicin ta hanyar diplomasiyya ba, amma ba za ta yi shawarwari da kungiyar Hezbullah ba, kuma wannan bai bayyana cewa Israi'ka za ta daina kai harin soja ba.

A sa'i daya kuma, babban sakataren MDD Kofin Annan ya ce, kwamitin sulh na MDD yana shirin tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kudancin Lebanon. A ran nan kuma babban sakataren kungiyar kawancen kasashen Larabawa ya nuna afakaice cewa, watakila kungiyar za ta karbi wannan shawara. Bi da bi ne Rasha da Amurka suka bayyana cewa, za su aika da wakilan musamman zuwa yankin gabas ta tsakiya domin gudanar da aikin sulhuntawa.(Danladi)