
Wakilinmu ya ruwaito mana labari cewa, a ran 17 ga wata, an yi taron tattaunawa a tsakanin shugabannin kungiyar kasashe G8 da na kasashe masu tasowa a birnin Saint Petersburg na kasar Rasha. A gun taron, an yi tattaunar musamman a kan batutuwa 4, wato samar da isasshen makamashi, da shawo kan cututtuka masu yaduwa, da ba da ilmi, da raya Afrika da sauransu. Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya halarcin taron, kuma ya yi wani jawabi a kai, inda ya yi bayani na musamman kan batun samar da makamashi lami lafiya a duk duniya, kuma ya gabatar da sabon ra'ayin makamashi na hadin kai don moriyar juna da samun bunkasuwa daga fannoni daban daban da ba da taimako ga juna don samun tabbaci.
A gun taron tattaunawa, da farko, Mr. Putin, shugaban kasar Rasha ya nuna gaisuwarsa, bayan haka kuma ya yi wani jawabi. Daga baya, shugabannin da suke hallartar taron sun yi musayar ra'ayoyinsu kan batuttuwan tattaunawa.
A cikin jawabinsa Mr. Hu Jiantao ya ce, muhimman abubuwan da aka tattauna a kai su ne inganta samar da makamashi, da shawo kan cututtuka masu yaduwa, da aikin samar da ilmi, da raya Afirka, wadannan suna dacewa da halin da ake ciki, kuma sun shafi makomar duniya. Warware wadannan matsaloli lami lafiya, wannan ya shafi da moriyar jama'a da kasashe daban daban, kuma ya shafi da makomar bunkasuwar al'umma.
Mr. Hu Jintao ya nuna cewa, ko wace kasa tana da ikon ingiza bunkasuwar kanta ta hanyar yin amfani da makamashi sosai, yawancin kasashe ba su iya samun tabbaci wajen inganta hanyar samar da makamashi, idan ba su hada kai da kasashen waje ba. Sabo da haka, ya kamata kasashen duniya su kafa da kuma bin sabon tsarin samar da makamashi na hadin kai don moriyar juna da samun bunkasuwa daga fannoni daban daban da ba da taimako ga juna don samun tabbaci, ban da wannan kuma ya kamata su mai da hankali kan yin kokari a fannoni uku, na farko shi ne karfafa hadin gwiwa kan raya makamashi don moriyar juna, na biyu shi ne kafa tsarin nazari da bunkasa fasahohin makamashi na zamani, na uku shi ne samar da yanayin siyasa mai kyau wajen samar da makamashi lami lafiya.
Bayan haka kuma, Mr. Hu Jintao ya bayyana muhimman abubuwan da ke cikin tsare-tsaren makamashi na kasar Sin, ya jadadda cewa, kasar Sin babbar kasa ce wajen yi amfani da makamashi, ita ce kuma wata babbar kasa mai fitar da makamashi. Kasar Sin za ta karfafa hadin kai da kasashe masu yi amfani da makamashi da wadanda ke fitar da makamashi, bisa manufar daidaitawa da samun moriyar juna, da kuma kiyaye kwanciyar hankali na makamashin duk duniya.
A cikin jawabinsa a rubuce, Mr. Hu Jintao ya bayyana matsayin da kasar Sin ke tsayawa kan batuttuwan shawo kan cututtuka masu yaduwa, da ba da ilmi, da raya Afrika da sauransu.
Mr. Putin, shugaban taron ya nuna cewa, dalilin da ya sa aka sanya muhimmanci kan batutuwan samar da isasshen makamashi, da shawo kan cututtuka masu yaduwa, da ba da ilmi, da raya Afrika, shi ne ko wace kasar ba ta iya magance da wadannan manyan kalubalen duniya da kanta. Bayan da shugabannin kasashe daban daban, da jami'an hukumomin duniya suka tattauna kan batuttuwan, dukansu suna ganin cewa, tilas ne a tafiyar da hadin kai a tsakanin kasashen duniya a dukan fannoni, da kuma daukar matakai masu amfani.
A gun liyafar abincin rana da Mr. Putin ya shirya bayan taron, Mr. Hu Jintao ya bayyana matsayin da gwamnatin kasar Sin ke tsayawa kan halin da zirin tekun Korea ke ciki, da shawarwari na Doha, da kuma sauran matsaloli. (Bilkisu)
|