A ran 18 ga wata, ministar harkokin waje ta kasar Isra'ila Tzipi Livni ta ta nuna ahabaice cewa, domin daidaita rikicin da ake yi a tsakanin Isra'ila da Lebanon, Isra'ila ba za ta yi adawa da girke sojojin kiyaye zaman lafiya a kudancin kasar Lebanon ba.
A ran nan a birnin Kudus, Malama Livni ta yi shawarwari da kungiyar da ke da mutane 3 ta MDD. Ta ce, makasudi na karshe na Isra'ila shi ne sojojin gwamnatin Lebanon su girke a kudancin Lebanon domin hana dakarun kungiyar Hezbullah su kai farmaki a kan Isra'ila. Amma sabo da a halin yanzu gwamnatin Lebanon ba ta da irin wannan kwarrewa, shi ya sa Isra'ila take son yin la'akari a kan sauran hanyoyi. Malama Livni ta ce, wannan bai bayyana cewa Isra'ila za ta rage matakin soja da take dauka a kan kungiyar Hezbullah a halin yanzu ba, dalilin da ta yi haka shi ne domin hana sake faruwar rikici tsakaninsu.
Mamban kungiyar da ke da mutane 3 ta MDD kuma manzon musamman na MDD mai kula da al'amuran shiyyar gabas ta tsakiya Terje Roed-Larsen ya ce, ya zama tilas a kafa wani tsarin siyasa domin sa kaimi ga bangarorin biyu da su daina rikicin.(Danladi)
|