Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-18 16:33:12    
Ya kamata a mai da hankali kan abincin da kananan yara suka ci, a lokacin da suke fama da tari

cri

Yanzu za mu soma gabatar muku da labarin da muka shirya muku. Mun ba da wasu shawarce-shawarce ga iyayen kananan yara game abincin da 'ya 'yansu suka ci, a lokacin da suke fama da tari.

Bayan da yara suka kamu da ciwace-ciwacen numfashi, an yi musu jinya, a lokacin nan, idan iyayensu sun mai da hankula kan kyautata abincin da suka ci, za a ba da taimako wajen warkar da tari.

Da farko, an shirya abinci ba tare da gishiri da mai da yawa ba, amma ya fi kyau a zabi abinci mai gina jiki, kuma yara sun iya hadiye su cikin sauki, kamarsu kunu tare da kayan lambu da romo da dai sauransu.

Na biyu kuma shi ne, an sa kaimi ga yara da su yi kokarin shan ruwa, kada a sha lemo a maimakon ruwan sha. Isasshen ruwa zai biya bukatar jikin yaran da suke fama da tari.

Na uku kuma shi ne, yara sun yi kokarin cin danyen kayan lambu da 'ya 'yan itatuwa. Danyen kayan lambu da 'ya 'ya itatuwa su kan ba da isassun gishiri na ma'adini da abubuwa masu gina jiki kamar bitamin, wadanda suka amfana wa warkar da tari. Haka kuma, cin kayan lambu da 'ya 'yan itatuwa da ke kunshe da tumatir da karas da kuma abincin da cike suke da bitamin na A ya kuma ba da taimako wajen warkar da hanyoyin numfashi na yara.

Na karshe dai shi ne, ya kamata yaran da suke fama da tari su magance cin abinci mai gishiri ko kuma mai zaki. Abinci mai gishiri zai tsananta tari, abinci mai zaki kuma zai haifar da kaki, shi ya sa, ya kamata yara su yi kokarin magancen cin irin wannan abinci. Sa'an nan kuma, kada yara su ci abinci mai yaji da soyayyen abinci da abinci mai sanyi da kuma abincin teku. Haka kuma, ya fi kyau a hana yaran da suke fama da tari su ci soyayyen gyada da iri na kankana da makamatansu.(Tasallah)