Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-18 16:30:40    
Shahararrun wuraren yawon shakatawa da ke gefunan hanyar dogo da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ta kasar Sin

cri

Lokacin da suke kan hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet, masu yawon shakatawa ba ma kawai suna iya jin dadin ganin babban tudun Qingzang ba, har ma suna iya dandana al'adun kabilar Zang da ke cike da addidi sosai.

Birnin Xining

Mafarin hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet shi ne birnin Xining, wanda tsohon birni ne da ke kan babban tudu, ya yi suna ne saboda gidan ibada na Ta Er da ke kwarin manyan duwatsu na Lianhua na gundumar Huangzhong ta birnin. Gidan ibada na Ta Er wuri ne da aka haifi dattijo Zong Kaba, wanda ya kafa darikar Gelu, kuma cibiya ce da masu bin addinin Lama ke tafiyar da addininsu a yankin arewa maso yammacin kasar. Babban ginin da ke cibiyar wannan gidan ibada shi ne fada mai suna Da Jin Wa, wadda ke da koren bango da kuma rufi mai launin zinare. Fadar da sauran tsoffin gine-gine sun nuna hadaddun fasahohin kabilun Han da Zang da kuma hali na musamman.

Tabkin Qinghai

Tabkin Qinghai yana arewa maso gabashin babban tudun Qingzang, shi ne takbi mai ruwan girishi mafi girma a duk kasar Sin. Tsawonsa ya kai mita 3260 daga lebur na teku. Tun daga watan Afril zuwa watan Yuli a ko wace shekara, dubban tsuntsaye ne ke yada zango a tsibiran da ke cikin wannan tabki, suna tafiya a cikin sararin samaniya, suna wasa a cikin ruwa, suna zaune a rairayin bakin tabkin, sun rera waka tare sai ka ce tsawa, an iya jin kukansu daga wuri mai nisa kilomiya sama da 10.

Birnin Ge'ermu

Sabon birnin Ge 'ermu yana cikin hamada, wanda nisan da ke tsakaninsa da tabkin Qinghai ya kai kilomita 800. Akwai tabkin gishiri mai suna Cha Er Han, wanda mafi girma a duk kasar a nan, lu'ulu'u na gishiri masu launuka iri daban daban akwai su ko ina a cikin wannan tabki. Idan ana rana, fuskar tabkin ta yi kamar wani babban madubi, ya fito da haske mai launin azurfa ko na shudi.

Yankin Keke Xili, inda babu mutane a ciki

Ma'anar Keke Xili a bakin 'yan kabilar Mongolia ita ce budurwa mai kyaun gani, da ke arewa maso yammacin babban tudun Qingzang, yana kuma tsakanin babban dutsen Kunlun da Tanggula, girmansa ya kai muraba'in kilomita dubu 83, matsakaicin tsayinsa ya kai fiye da mita 4600 daga lebur na teku. Keke Xili yana daya daga cikin shiyyoyin kiyaye halitta na kasar Sin, wanda ya fi girma da tsawo, haka kuma, an fi samun naman daji iri daban daban a nan. Lokacin da ake wucewa a Keke Xili, ana iya ganin bareyi iri na Tibet suna gudu, sa'an nan kuma, ayarin motoci masu yawa suna zuwa Lhasa don jigilar da kayayyaki.

Mafarin kogin Yangtse

Kogin Tuotuo mafari ne na kogin Yangtse na gaskiya, ruwa ya tashi daga kan babban dutse na Gela Dandong na manyan duwastu na Tang Gu La, wanda tsawonsa ya kai mita 6621 daga lebur na teku. A kudu maso yammacin babban dutse na Gela Dandong akwai kogin kankara na Jianggen Diru, a karshen wannan kogin kankara akwai hasumiyoyin kankara da yawa.

Fili mai ciyayi na Qiangtang da ke arewacin Tibet

Bayan da aka ketare babban dutse na Tang Gu La, sai a gamu da fili mai ciyayi na Qiangtang da ke arewacin Tibet. A nan akwai Shenzha, wanda fada ce ga tsuntsaye, da Shuanghu, wanda Aljanna ce ga naman daji, da tabkin Na Mu Cuo mai tsarki da dai sauransu. Tabkin Na Mu Cuo tabki ne mai ruwan gishiri da ya fi tsawo daga lebur na teku a duk duniya, tsawonsa ya kai mita 4718 daga lebur na teku, ya zama na farko a cikin jerin tabkuna guda 3 masu tsarki na Tibet.

Lhasa

Birnin Lhasa shi ne karshen haryar dogo da ta hada Qinghai da Tibet. Fadar Potala da ke cikin wannan birni fada ce da ta fi tsawo daga lebur na teku a duk duniya, wadda ta shahara ne saboda tarihinta mai dogo da kuma darajar fasaharta. An ajiye kakayyakin tarihi da zane-zanen masu daraja da yawa da aka yi a kan bangwayen wannan shahararriyar fada.(Tasallah)