Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-18 16:28:23    
Gidan ibada na Da Zhao

cri

Mutum-mutumi na Sakyamuni da aka girmama shi a gidan ibada na Da Zhao gimbiya Wencheng ta daular Tang ce ta shiga cikin Tibet tare da shi, dalilin da ya sa aka mayar da Lhasa a matsatyin wuri mai tsarki yana da nasaba da wannan mutum-mutumi. A farko dai, an kira wannan gidan ibada 'Resa', daga bisani kuma an kira wannan birni 'Resa', sannu a hankali, sunan wannan birni ya canja zuwa Lhasa. A cikin shekara da shekaru, gidan ibada na Da Zhao ba ma kawai cibiyar jihar Tibet a fannin manyan ayyukan addinin Buddha ba, har ma fada ce mai tsarki a cikin zukatan dukan masu bin addinin Buddha har abada.

An fara gina gidan ibada na Da Zhao a karni na 7, wanda an ce, gimbiya Chizun ta kasar Nepal da gimbiya Wencheng ta daular Tang ta kasar Sin su ne suka yi jagorancin gina shi cikin hadin gwiwa, wandanda kuma su ne matan sarkin Tibet Srong-brtsan-sgam-po. An taba kiransa 'Resa' da 'Jixie'. Amma a karni na 9, an canja sunansa zuwa gidan ibada na Da Zhao, wato fada ce da aka ajiye littattafan addini. A zamanin daular Qing kuma, an taba kiransa da suna gidan ibaba na Yi Ke Zhao. Gidan ibada na Da Zhao tsohon gini ne da aka yi da katako a jihar Tibet, wanda aka kwaiwakyi salo iri na gine-gine na daular Tang, don haka gidan ana da sigar musamman ta kabilun Han da Zang. Da ma gidan ibadan nan karami ne, amma Dalailama na 5 ya kyautata shi a karni na 17, yana ci gaba da kasancewa har zuwa yanzu. Babbar fada ta wannan gidan ibada yana da banaye 4, an gina shi bisa salo na kabilar Han, amma an yi ado ga rufi da kan ginshikai bisa salo na kabilar Zang. A cikin bene na farko na babbar fadar, akwai wani mutum-mutumi na zinare mai daraja na Sakyamuni, wanda ya kafa addinin Buddhism. Gimbiya Wencheng ta shiga cikin Tibet tare da wannan mutum-mutumi. An ajiye mutum-mutumi na wannan ginbiya da sarki Srong-brtsan-sgam-po a cikin bene na biyu. An yi zane-zane a kan bangwayen wannan fada da kuma hanyoyin cikin fadar, fadin zane-zanen da aka yi ya kai muraba'in mita fiye da dubu 2 da dari 6 gaba daya, wadannan zane-zane sun hada da addinin Buddhism da shahararrun mutanen tarihi da kuma labarunsu.(Tasallah)