Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-17 21:31:07    
An sami sakamako mai kyau wajen tsimin ruwa a kasar Sin

cri

Yawan albarkatun ruwa da ke akwai a kasar Sin ya dauki kashi 7 cikin dari bisa na duk duniya. Amma kasar Sin ta yi amfani da wadannan albarkatun ruwa wajen ciyar da mutane da yawansu ya kai kashi 21 cikin dari bisa na duk duniya. A sakamakon karuwar yawan mutane da bunkasuwar tattalin arziki da sauri, za a kara fama da karancin ruwa a kasar Sin. Sabo da haka a shekarun nan da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da ra'ayin raya zaman jama'a ta hanyar tsimin ruwa. Manufar ra'ayin nan ita ce kara daga matsayin yin amfani da albarkatun ruwa.

Birnin Tangshan wani birnin masana'antu ne mai muhimmanci a arewacin kasar Sin. Ko da yake ayyukan haka kwal da na narke karafa da yin tangaran da sauransu na wannan birni sun shahara sosai a duk kasar Sin, amma ana bukatar ruwa mai tarin yawa wajen gudanar da wadannan ayyuka. Sabo da haka hukumar birnin nan ya gabatar da manufar gina birnin nan da ya zama birni mai tsimin ruwa. Wani tsaurarran mataki da aka dauka a birnin shi ne kara daga matsayin sake yin amfani da gurbataccen ruwa.

Kamfanin haka kwal na birnin Tangshan yana gudanar da mahakan kwal guda 11 wadanda ke fitar da gurbataccen ruwa da yawansu ya kan kai cubic mita miliyan 100 a ko wace shekara. Don haka kamfanin nan ya kafa wata ma'aikatar tace gurbataccen ruwa a shekarar 1992. Malam Guo Hai, mataimakin shugaban wannan ma'aikata ya bayyana cewa, "yawan kudi da ake kashewa wajen tace gurbataccen ruwa Tan daya ya kai kudin Sin Yuan 1. 32. Amma idan an jawo ruwa mai nauyin tan daya daga rijiya mai zurfi, to, za a kashe kudin Sin Yuan 2.12. Yanzu, ma'aikatarmu ta kan tace gurbataccen ruwa mai nauyin tan miliyan 3.6 da mahakan kwal ke fitarwa a ko wace shekara, ta haka ba ma kawai muna iya tsimin ruwa mai tarin yawa ba, har za mu iya tsimin kudin Sin Yuan Miliyan 2.9 a ko wace shekara."

Malam Guo Hai ya kara da cewa, mu iya yin amfani da gurbataccen ruwa da aka tace wajen shayar da bishiyoyi da ciyayi, da zuba shi cikin kwari don kayatar da muhalli da dai sauransu. Ta haka mun daga matsayinmu sosai wajen yin amfani da albarkatun ruwa.

Rawayen Kogi wani babban kogi ne da ke malala a arewacin kasar Sin. A jihar Ningxia ta kabilar Hui mai ikon aiwatar da harkokin kanta da jihar Mongoliya ta gida mai ikon aiwatar da harkokin kanta, a kan jawo ruwa mai tarin yawa daga rawayen kogi don gudanar da ayyukan samar da kayayyaki a ko wace shekara.

A sakamakon ci gaba da ake samu wajen bunkasa aikin masana'antu da sauri a jihohin nan biyu, yawan ruwa da ake bukata ya karu da sauri musamman a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce. A cikin irin wannan hali ne, tun daga shekarar 2003, masana'antu na jihohin nan biyu sun kashe makudan kudade wajen kyautata ayyukan ban ruwa domin neman tsimin ruwa. Daga baya sai aka samar da ruwa da aka yi tsiminsa daga aikin noma ga masana'antun nan. Malam Hu Siyi, mataimakin ministan tsare ruwa na kasar Sin ya ce, "an daidaita yawan ruwa da ake amfani da shi a tsakanin birane da kauyuka ta hanyar nan. Ta haka an sami sakamako mai kyau wajen yin amfani da albarkatun ruwa sosai, kuma an ba da tabbaci ga samar wa birane da kauyuka da isasshen ruwa don bunkasa harkokin tattalin arziki da na zaman jama'a. "

A jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai ikon aiwatar da harkokin kansu da ke a arewa maso yammacin kasar Sin, ana fama da karancin ruwa sosai. Sabo da haka tun daga shekarar 1996, aka fara daukan matakai daban daban wajen shayar da gonaki ta hanyar tsimin ruwa. Malam Su Jun, jami'in hukumar birnin mai suna "Shihezi" na jihar mai kula da harkokin tsimin ruwa ya bayyana cewa, "ya zuwa yanzu dai, fadin gonaki da muke shayar da su ta hanyar tsimin ruwa ya kai kadada dubu 120. Tsire-tsire da ake noma a gonakin nan sun hada da auduga da tumatir da innabi da sauransu. Mun sha yin girbin amfanin gona mai armashi a shekarun nan da suka wuce, musamman yamfanin gona da muka girba a shekarar bara ya yi armashi sosai har ba a taba samun irinsa a da. " (Halilu)