Yawancin mutanen kabilar Du Long suna da zama a bakin kogin Du Long, wasu suna da zama a wuraren da ke bakin kogin Nu. Bisa kididdigar da aka yi a shekara ta 2000, yawan mutanen kabilar Du Long ya kai 7426. Suna da yaren Dulong, amma babu kalma.
Kafin kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, ko da yake kabilar Du Long ba ta da sana'ar narke karafa, amma domin tana da dangantakar siyasa da tattalin arziki da kabilun Tibet da Nasi da Bai kuma da kabilar Han cikin dogon lokacin da ya wuce, a kan shigar da wukake da gatura a gidajen kabilar Du Long daga wadannan kabilu domin aikin gona.
Amma lokacin da aka 'yantar da wurin da kabilar Du Long take da zama a watan Yuli na shekarar 1949, mutane na da ikon mallakar dukiyoyinsu a kabilar Du Long. Kowane gida yana da wukake da gatura nasu.
Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, jama'ar kabilar Du Long sun shiga sabon lokaci. A ran 1 ga watan Oktoba na shekarar 1956, an kafa gandummar Gongshan ta kabilun Du da Nu. Jama'ar kabilar Du sun samu ikon mallakar zaman rayuwarsu da kansu kamar yadda sauran kananan kabilun kasar Sin suka samu. Jam'iyyar kwaminis ta kasar sin da gwamnatin kasar Sin sun kuma tsai da kudurin ba da taimako ga kabilar Du Long wajen neman bunkasuwarta domin kawar da halin fama da talauci da kabilar Du Long take ciki a wancan lokaci. An gudanar ayyukan ban ruwa, an sari sabbin gonaki da kyautata hanyoyin aikin gona a yankunan da kabilar Du take da zama. Sabo da haka, yawan amfanin gona da mutanen kabilar Du suka samu ya samu karuwa a kai a kai a kowace shekara. Bugu da kari kuma, mutanen kabilar Du Long sun raya sana'ar kiwon fatauci. Gwamnatin wurin ta gina dam na samar da wutar lantarki da shimfida hanyar mota a yankin da mutanen kabilar Du Long suke da zama. Yanzu, yaran da suka kai kashi 85 cikin kashi dari na kabilar Du Long sun samu izinin shiga makarantun firamare.
Mutanen kabilar Du Long sun fi son sanya tufafin da suka yi da kansu. Kuma muhimman abinci da suke ci ya kunshi shimkafa da garin alkama. A da, domin ba su iya samun isassun shimkafa da garin alkama, su kan yi farautar namun daji da cin naman dabbobi. Mutanen kabilar Du Long sun fi son shan giya irin ta shimkafa da suka yi da kansu, kuma suna son shan ti da shan taba. A cikin wani gidan mutanen kabilar Du Long, dukkan iyalai suna da zama tare. Ko yara sun yi aure, suna kuma zama da iyayensu tare. Idan akwai yara da yawa, amma babu isassun dakuna, sai a gina sabbin dakunan da ke kusa da gidan iyayensu.
Mutanen kabilar Du Long suna da sha'awar waka da raye-raye. Lokacin da suke aiki da yin girbi da farauta da gina gidaje da neman aure ko shirya shagulgula, su kan rera wakoki da yin raye-raye domin bayyana fatansu.
Game da auren kabilar Du Long, ko da yake, yanzu, kowane namaji ya iya auren mace daya. Amma domin a da, kabilar Du Long tana da al'adar cewa, kowane miji ya iya auren mata da yawa, har yanzu, wasu maza suna auren mace fiye da daya.
Bugu da kari kuma, mutanen kabilar Du Long suna girmama halittu. Suna ganin cewa, dodanni suna kasancewa a cikin iska da ruwan sama da tsawa da tuddai da manyan itatuwa suna da rai. (Sanusi Chen)
|