Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-17 20:49:31    
Yadda aka shimfida hanyar dogo ta Qingzang

cri

A ran 1 ga watan Yuli ne shekarar da muke ciki, hanyar dogo ta Qingzang, wato tsakanin jihohin Qinghai da Tibet na kasar Sin, wadda ta fi tsayi daga leburin teku a duniya ta fara yin gwajin sufurin fasinjoji. Sabo da fuskantar matsaloli masu tsanani kwarai da gaske kamar dusar kankara da rashin iska a kan tudun Qingzang da dai sauransu, kafin wannan wasu kwararrun kasashen waje sun taba tabbatar da cewa, tabbas ne ba za a iya shimfida hanyar dogo a kan tudun Qingzang ba. Amma masu shimfida hanyar dogo na kasar Sin sun haye matsaloli iri iri, a karshe dai sun ci nasarar shimfida wannan hanyar dogo da ta ratsa tudun, wato kololuwar tsaunukan duniya. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan yadda aka shimfida hanyar dogo ta Qingzang.

Kamar yadda aka rera a cikin wannan wakar da ta karbuwa sosai a tudun Qingzang na kasar Sin, wannan wata hanyar dogo ce da ke cikin sararin sama. Lokacin da aka shimfida hanyar dogo ta Qingzang, an fuskanci wahaloli iri daban daban, wadanda suka fi tsanani su ne kasa mai dusar kankara da kuma rashin iska a kan tudun.

Hanyar dogo da aka fara gwajin yin amfani da ita dazun nan wata hanya ce da take tsakanin birnin Germu na lardin Qinghai da birnin Lhasa na jihar Tibet, kuma tsawonta ya kai kilomita 1142, amma kusan rabin hanyar za ta ratsa yankin dusar kankara. Malam Lin Lan na kamfanin shimfida hanyoyin dogo na kasar Sin wanda ke kula da aikin shimfida hanyar dogo ta Qingzang ya gaya wa wakilinmu cewa, matsalar kasa mai dusar kankara ta taka mumunar rawa sosai ga shimfida hanyar,

"idan muka shimfida harsashin ginin hanyar dogo a kan kasa mai dusar kankara, to idan lokacin hunturu ya yi, dusar kankara ta kan kumbura, ta haka za ta ba da tasiri ga gine-ginen da aka gina su a kan ta, amma lokacin zafi ya yi, dusar kankara ta kan narke, kuma girmanta zai ragu, ta haka harsashin gini na hanyar dogo zai yi kasa kasa. "

To, yanzu bari mu ga yadda aka warware matsalar yayin da ake shimfida hanyar dogo ta Qingzang. Masu shimfida hanyoyin dogo na kasar Sin sun gabatar da wani shiri, wato sun ajiye dutse da kaurinsa ya kai fiye da mita guda tsakanin doron kasa da kasa mai dusar kankara, ana kiran irin wannan dutse da suna "airconditioner na kasa". Lin Lan na kamfanin shimfida hanyoyin dogo ya bayyana cewa, a hakika dai irin wannan "air conditioner na kasa" harsashin ginin hanyar dogo ne na musamman.

Wata dabara daban wajen warware matsalar kasa mai dusar kankara ita ce a gina gadoji a maimakon hanyoyi. Tsawon gadojin da ke cikin hanyar dogo ta Qingzang ya zarce kilomita 150, kuma wannan karo na farko ne a duniya da aka gina gadoji da dimbin yawa a maimakon hanyoyi.

Ban da matsalar dusar kankara, masu shimfida hanyar dogo ta Qingzang sun fuskanci matslar muhallin halittu mai tsanani sosai. Yadda aka tabbatar da lafiyar jikinsu ya zama wata matsala da ake bukatar warware ta cikin gaggawa. A filin shimfida hanyar dogo ta Qingzang, yawan sanyi ya kai 45 kasa da sifiri, kuma a cikin kwanaki 100 zuwa 160 na ko wace shekara akwai iska mai karfi sosai. Ban da wannan kuma rashin iska a kan tudun Qingzang wata matsala ce da ta fi tsanani. A cikin dogon rami na dutsen Fenghuo na hanyar dogo ta Qingzang, wadda ta fi tsayi daga leburin teku a duniya, yawan iskan Oxygen ya kai kashi 50 cikin dari idan an kwatanta shi da na sauran wurare. Kuma rashin iska a kan tudun ya kawo babban cikas ga shimfida hanyar dogo, a waje daya kuma shi batu ne da masu shimfida hanyar dogo suka fi damuwa da shi. Shugaban masu gina dogon rami na dutsen Fenghuo Ren Shaoqiang ya gaya wa wakilinmu cewa,

"sabo da ana karancin iskar Oxygen sosai a kan tudun, shi ya sa dukkanmu muna shan wahala. Kuma kafin mu je tudun, muna jin tsoro sosai."

Domin warware matsalar rashin iska a kan tudun, na farko, ko wane mai shimfida hanyar dogo ta Qingzang yana dauke da wata kwalbar iskan Oxygen yayin da suke yin aiki, amma nauyin kwalbar ya sa karfin jikin masu shimfida hanyar dogo ya ragu sosai. Sabo da haka kamfanin shimfida hanyar dogo ya dauki sabbin matakai, wato an gina manyan tasoshin samar da iskan Oxygen domin samar da iskan Oxygen ba tare da katsewa ba. Kuma sabo da wannan sabuwar dabara da aka yi amfani da ita wajen samar da iskan Oxygen, yawan mutane da aka kamu da ciwon tudun ya ragu da kashi 94 cikin dari. An kafa tasoshin samar da iskan Oxygen fiye da goma a hanyar dogo ta Qingzang gaba daya, ta yadda aka kafa wani tushe mai kyau wajen shimfida hanyar dogo ta Qingzang lami lafiya da kuma warware rashin iska a kan tudun.(Kande Gao)