Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-17 16:40:41    
Ko kungiyar kasashe 8 sun riga sun cika alkawaransu da suka yi wa Afrika

cri
A gun taron koli na kungiyar kasashe 8 da aka kira a Scotland a shekarar da ta wuce, a cikin kokarin da Mr. Blair, firayin ministan kasar Ingila ya yi, kungiyar kasashe 8 ta yi alkawura 3 ga Afrika, wato soke bashi na kasaske masu fama da talauci, da kara ba da taimako, da kuma kafa wani tsarin ciniki mai adalci ga kasashen Afrika. Yanzu, shekara daya ta wuce, shugabannin kasashen kungiyar 8 za su sake taruwa a St. Petersburge. To, ko sun riga sun cika alkawaransu?

Da farko, bari mu duba batun soke albashi.

A cikin shekara daya, kungiyar kasashe 8 ta soke bashi na kasashe 14 na Afrika, kuma ta rage bashi sosai na kasashe 8 na Afrika. Bayan haka kuma, kungiyar asusun ba da lamuni ta duniya, wato kungiyar IMF, da bankin duniya sun ba da sanarwar soke bashi dollar Amurka fiye da biliyan 40 ga kasashe 40 da suka fi talauci a duniya.

Ko da ya ke bashin da aka soke bai kai kashi daya cikin dari bisa na jimlar bashin da ake bin kasashen Afrika ba, amma an riga an ga sakamakon da aka samu sabo da rage albashi. Kamar misali, kasar Zambia, wadda ta riga ta kau da hargitsin albashi ta riga ta soma tsarin ganin likita ba tare da biyan kudi ba a cikin kauyukka daga watan Afril na shekarar da muke ciki.

Yanzu, bari mu ga halin kara ba da taimako da ake ciki.

Yanzu, akwai kasashe 28 na Afrika suna dogara da taimakon da aka ba su daga kasashen waje sosai. Sabo da haka, a shekarar da ta wuce, kungiyar kasashe 8 ta yi alkawari cewa, za ta ba da taimakon kudi dollar Amurka biliyan 25 ga Afrika a ko wace shekara, kuma za ta kara yawansu zuwa biliyan 50 a ko wace shekara kafin shekarar 2010. Amma, a gun babban taro na "ba da taimako domin samu bunkasuwa", wakilin kasar Nijeria ya ce, "ba a ga wani ci gaba da aka samu ba a wajen wadannan alkawara ba".

Bisa kididdigar da aka yi an ce, yawan kudin ba da taimako da kungiyar kasashe 8 ta bayar bai kai na sauran kasashe masu sukuni ba. A cikin kasashe 8, yawan kudin ba da taimako da kasar Italiya ta bayar ya karu kashi 46 cikin dari, yawan kudin da kasashen Amurka, da Canada, da Japan suka bayar ya karu kashi 16, da kashi 18, da kashi 14 cikin dari. Amma, yawan kudin nan da kasashen Faransa, da Jamus, da kuma Ingila suka bayar a cikin shekarar da ta wuce bai kai na da ba. Ko da ya ke kungiyar za ta iya cika alkawarinta na ba da taimakon kudi dollar Amurka biliyan 50 kafin shekarar 2010, amma yawan kudin ya kai kashi 0.36 cikin dari bisa na GDP nasu, amma a shekaru 30 da suka wuce ta yi alkawari cewa, yawan kudin ba da taimako da za ta bayar zai kai kashi 0.7 cikin dari bisa GDP nasu. Yanzu, kullum kasashen yamma suna kutsa kai cikin sha'anonnin gida na kasashen Afrika, haka kuma su kan rage taimako sabo da tare da sharuda iri daban daban.

A karshe, bari mu ga halin kafa tsarin ciniki mai adalci ga kasashen Afrika.

Kasashen Afrika da yawa suna ganin cewa, cire kangin cinikayya na kasashe masu sukuni, wannan ne abin muhimmanci wajen kau da talauci na Afrika. Bisa kididdigar da aka yi an ce, idan kasashen Afrika sun kara kashi daya cikin dari a cikin ciniki na duk duniya, to moriyar da za su samu za ta ninka sau 5 bisa na taimakon da suka samu daga kasashen waje. Amma, yanzu Afrika tana da kashi 2 cikin dari kawai a cikin cinikin duniya kawai. A gun taron koli na kungiyar kasashe 8 da aka shirya a shekarar da ta wuce, babban jami'in kungiyar WTO ya roki kungiyar kasashe 8 da su kawo karshen ciyewa da aka samu a shawarwarin ciniki na duniya na Doha, domin ba da taimako ga kasashe masu fama da talauci. Yanzu, shekara 1 ta wuce, ba a sami ci gaba wajen shawarwarin ba, har ma bangarori daban daban ba su sami ra'ayi daya ba kan yadda yarjejeniyar ciniki mai ba da amfani ga kasashe masu talauci ya ke kamar yadda ya kamata.

Bisa matsayinta na wani muhimmin tsarin daidaituwa na kasashe masu sukuni, kungiyar kasashe 8 suna iya ba da muhimmin taimako a cikin harkokin siyasa da tattalin arziki na duniya. Nan gaba, ya kamata kungiyar ta mai da hankali sosai kan aiwatar da alkawuranta, haka kuma kasashen Afrika za su iya samu hakikanin moriya, da kuma samu hanyar kau da talauci da sauri. (Bilkisu)