Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-15 18:14:58    
Kwamitin sulhu ya bayyana shirin kasashe shida dangane da batun nukiliyar Iran

cri
A ran 13 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya bayyana shirin da kasashen Amurka da Rasha da Sin da Birtaniya da Faransa da kuma Jamus suka gabatar a watan Yuni na shekarar da muke ciki don neman daidaita batun nukiliyar Iran.

Shirin dai ya nuna goyon baya ga hakkin da Iran ke da shi na bunkasa makamashin nukiliya don amfanin jama'a bisa 'yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya', kuma ya nuna goyon baya ga kafa tashar na'urar 'light water reactor' a kasar Iran ta hanyar yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa, kuma masana'antun tace sidanarin Uranium na Rasha ce za su bayar da makamashi ga Iran a kai a kai. Ban da wannan, shirin ya kuma gabatar da jerin matakai don sa kaimi ga Iran, alal misali, mai yiwuwa ne za a yi watsi da kayyade na'urorin jiragen saman fasinja da kayayyakin sadarwa da masana'antun Amurka da gamayyar Turai suke fitarwa zuwa Iran, kuma za a mara wa Iran baya wajen shiga kungiyar WTO da dai sauransu.(Lubabatu Lei)