 A ran 16 da ran 17 ga wata, Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin zai halarci taron tattaunawa da za a yi a tsakanin shugabannin kungiyar kasashe G8 da na kasashe masu tasowa a birnin Saint Petersburg na kasar Rasha. A gun taron, za a tattauna musamman a kan batutuwan samar da isasshen makamashi, da shawo kan cututtuka masu yaduwa, da ba da ilmi, da raya Afrika da ciniki da sauransu. Sa'an nan kuma za a tattauna a kan batutuwan mayar da tattalin arzikin duniya da ya zama bai daya, da yaki da ta'addanci, da hana yaduwar manyan makaman karen dangi, da sauran batutuwan duniya da na yankuna da ke jawo hankulansu duka. Shugaba Hu Jintao zai bayyana matsayin kasar Sin da ra'ayoyinta a kan wadannan manyan batutuwa. A lokacin da ake yin taron tattaunawa a tsakanin shugabannin manyan kasashe masu sukuni da masu tasowa a wannan gami, muryar kasar Sin tana jawo hankulan mutane sosai, bisa matsayinta na kasa mai tasowa kuma mafi girma a duniya.
A gun taron maname labaru da aka yi a kwanakin baya, Mr Cui Tiankai, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin ya bayyana ra'ayinsa a kan hulda a tsakanin kasar Sin da kungiyar G8, kuma yana fatan alheri ga taron tattaunawar da za a yi nan gaba kadan. Ya ce, "kasar Sin tana dora muhimmanci ga rawar da kungiyar G8 ke takawa. Hadin kai a tsakanin kasar Sin da kungiyar G8 yana dacewa da moriyarsu duka, kuma yana da amfani ga samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasuwa a duniya. Wannan ne karo na uku da shugaba Hu Jintao zai halarci taron tattaunawa a tsakanin shugabannin kungiyar G8 da na kasashe masu tasowa. Muna fatan taron zai iya nuna abubuwa da ke jawo hankulan bangarori daban daban cikin daidaituwa, musamman ma muryar kasashe masu tasowa, ta yadda za a ciyar da hadin kan kasa da kasa gaba a fannoni daban daban. "

Kasar Sin kasa ce mai tasowa kuma mafi girma a duniya. Sabo da haka halartar taro da shugaban kasar Sin zai yi, da matsayin kasar Sin da ra'ayinta suna jawo hankulan mutane sosai. Mr. Cui Tiankai ya bayyana cewa, "a ran 17 ga wata, shugaba Hu Jintao zai halarci cikaken taron tattaunawa da liyafar cin abincin rana, inda zai bayyana ra'ayoyin kasar Sin a kan halin da ake ciki yanzu a duniya, kuma zai bayyana matsayin kasar Sin da ra'ayoyinta a kan batutuwa da za a tattauna a kai a gun taron dangane da samar da isasshen makamashi, da shawo kan cututtuka masu yaduwa, da ba da ilmi da raya Afrika da sauransu. Haka zalika shugaba Hu Jintao zai halarci ganawar da shugabannin kasashe masu tasowa shida kamar Sin da Indiya da Brazail da Afrika ta Kudu da Maxico da Kongo Brazzaville za su yi a tsakaninsu, inda zai bayyana ra'ayoyin kasar Sin a kan inganta hadin guiwa a tsakanin kudu maso kudanci da hadin guiwa a tsakanin kasa da kasa don samun bunkasuwa, kuma zai yi bayani a kan hadin guiwar da ake yi tsakanin Sin da kasashen Afrika. Ban da wadannan kuma shugaba Hu Jintao zai halarci ganawar da za a yi a tsakanin shugbannin kasashen Sin da Rasha da Indiya, zai gana da sauran shugabannin kasashe da abin ya shafa, inda za su yi musanyar ra'ayoyinsu a kan huldar da ke tsakaninsu da batutuwan duniya da ke jawo hankulansu duka."
Dangane da tambayar da aka yi ko kasar Sin tana la'akari da shiga cikin kungiyar G8, Madam Jiang Yu, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta ce, "a halin yanzu kasar Sin kasa ce mai tasowa. Ra'ayin kasar Sin shi ne kasashe masu sukuni da masu tasowa su yi hadin kansu cikin daidaici, su taimaki juna don magance kalubale da suke fuskanta a duniya. Muna son ci gaba da tattauna da hadin guiwa a tsakaninmu da kungiyar G8 bisa ka'idojin daidaici don moriyar juna. " (Halilu)
|