Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-14 18:27:39    
'Yan wasan kwallon tennis na kasar Sin sun ci nasara a kasaitacciyar gasa

cri

A da, mutane sun yi zaton, cewa, zakaran kasaitacciyar gasa ta wasan kwallon tennis yana can nesa ba kusa ba daga kungiyar wasan kwallon tennis ta kasar Sin saboda ta samu budin yalwa a wannan fannin wasa cikin gajeren lokaci. Amma tun daga shekarar 2004 zuwa shekarar 2006 wato lokacin da bai cika shekaru 3 ba, masu sha'awar wasan kwallon tennis na duk duniya suka gano kwaram, cewa ashe Sinawa suna kusa kusa da wannan zakara. A gun wasan tsakanin mata biyu-biyu na budaddiyar gasar wasan kwallon tennis da aka kawo karshenta a ran 9 ga watan nan, agogon wurin a Wimbledon na kasar Burtaniya, ' yan wasa su Zhenjie da Yanzi na kasar Sin sun lallasa abokan karawarsu da ci biyu da daya, wato ke nan sun dauko kofin zakaran Wimbledon ga kasar Sin a karo na farko, kuma wannan kofi na biyu ne na kasaitacciyar gasa da suka ci bayan da suka zama zakaru a gun budaddiyar gasar wasan kwallon tennis da aka yi a kasar Australiya a farkon shekarar da muke ciki.

A gun taron wasannin motsa jiki na Olympics da aka yi a Aden na kasar Girka a shekarar 2004, ' yan wasa su Li Ting da Sun Tiantian na kasar Sin sun zama lambawan a wasan da aka yi tsakanin mata biyu-biyu. Lallai wannan labari ya firgita duk duniya da kuma fadakar da mutane akan cewa ' yan wasan kwallon tennis na kasar Sin sun samu babban ci gaba.

Ma'anar kasaitacciyar gasa tana nufin, cewa budaddun gasanni 4 ne da akan shirya a duk tsawon shekara a kasashe 4 wato Australiya, da Faransa, da Wimbledon na Burtaniya da kuma Amurka. Wadannan budaddun gasanni 4, dauwamamun gasanni ne dake bisa matsayin ci gaba a duniya wadanda kuma akan yi su ne cikin zazzafan hali, wato ke nan suna wakiltar matsayin koli na duniya a wasan kwallon tennis a halin yanzu.

Bayan da 'yan wasa mata su Zhenjie da Yanzi suka zama zakaru a gun gasar da aka yi a Wimbledon, sai kafofin watsa labaru na kasashen Turai suka buga babban take ga nasarorin da 'yan wasa mata na kasar Sin suka samu. Wakilinmu ya ruwaito mana labari daga Wimbledon, cewa :

' Wata tashar wasan motsa jiki mafi girma ta Turai ta sharhanta, cewa 'yan wasa mata su Zhenjie da Yanzi sun zama 'yan wasa guda biyu na farko na kasar Sin da suka zama lambawan a tarihin wasan kwallon tennis tsakanin mata biyu-biyu na Wimbledon. Lallai wannan ya gwada babban karfin da Sinawa suke da shi na samun nasara a duniya'.

Babu tantama, 'yan wasan kwallon tennis na mata na kasar Sin sun rigaya sun cimma matsayin duniya. A sa'i daya kuma, a fannin irin wannan wasa na tsakanin mace da mace, ai ba a tafi an bar shi baya ba. ' Yar wasa mai suna Li Na ta kafa tarihi har ta shiga cikin jerin 'yan wasa guda 8 masu karfi na wasan kwallon tennis na Wimbledon a wannan shekara.

Mr. Jiang Hongwei, mai koyar da 'yan wasan kwallon tennis na kasar Sin ya fadi albarkacinsa kan babban ci gaban da 'yan wasa Sinawa suka samu. Ya futa ,cewa: 'Yanzu, 'yan wasa na kasar Sin sun samu babban ci gaba har sun kama matsayin gurabe 10 na farko a duniya a wasan kwallon tennis na tsakanin mata biyu-biyu; a fannin wasan tsakanin mace da mace ma, wata 'yar wasa ta kama matsayin gurabe 30 na farko a duniya. Ya kamata su ci gaba da yin kokari domin kafa sabon tarihi a gun irin wannan wasa'.

Jama'a, abun da da'irar wasan kwallon tennis ta kasar Sin ta fi mai da hankali a kai, shi ne 'yan wasan kasar Sin su kara karfi da gaske wajen buga kwallon. Mr. Jiang Hongwei ya fadi, cewa :

'Kada a kara barin sauran mutane su yi zaton cewa wai 'yan wasan kasar Sin sun yi sa'a ne kawai wajen samun lambar zinariya. Wajibi ne 'yan wasan su nuna himma da kwazo wajen kara samun karfi a kuma dabarun buga kwallon, ta yadda za su samu kyakkyawan sakamako a gun wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008'.( Sani Wang )