Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-13 21:18:30    
Ya kasance da hadin gwiwa kawai a tsakanin kasashen Sin da Afirka, babu barazana

cri
'Jama'ar kasar Sin sahihan abokan jama'ar Afirka ne har abada. Bunkasa huldar da ke tsakaninta da Afirka da kasar Sin ke yi, ba wai kamar yadda wasu sun ce domin albarkatun kasa na Afirka ba.' Wannan furucin da firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi yayin da yake yin ziyara a kasashen Afirka 7 a kwanan baya, ya sami amincewa daga kasashen Afirka baki daya.

Bana shekara ce ta cikon shekaru 50 da aka bude huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da kasashen Afirka. Shekarun nan 50 da suka wuce shekaru ne da kasar Sin ta taimaka wa Afirka wajen kara karfinsu da kuma ingiza bunkasuwarsu bisa karfin kansu, haka kuma shekaru ne da kasashen Afirka suka bai wa kasar Sin babban goyon baya a kan manyan al'amuran duniya masu yawa.'

'Har kullum dai, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka a kan bai wa 'yan uwanta na Afirka taimako bisa karfinta kuma ba tare da ko wane irin sharadin siyasa ba.' Abubuwa da yawa ne suka tabbatar da wannan kalamin da firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi a gun bikin bude taron dandalin tattaunawar harkokin kasuwanci na farko da ke tsakanin Sin da Afirka ta kudu: yawan ayyukan da kasar Sin ta ba da taimako wajen aiwatar da su a nahiyar Afirka don bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma na yankin ya kai kusan 900, kuma a cikin shekaru 6 da suka wuce tun bayan da aka kafa dandalin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, kasar Sin ta riga ta soke basussukan kasashen Afirka 31 wadanda yawansu ya kai kudin Sin yuan biliyan 10.5. A cikin shekaru 3 da suka wuce kuma, kasar Sin ta horar da kwararru iri iri kusan dubu 10 ga kasashen Afirka, kuma ba tare da sun biyan kudi ba. Sa'an nan likitocin kasar sin dubu 16 sun warkar da masu ciwo na Afirka kusan miliyan 240.

Har kullum dai, taimako shi ne taimako ga juna. Kasar Sin ba ta taba jin shakkun yin shelar bukatar Afirka ba. Tsohon shugaban kasar Sin Mao Zedong ya taba cewa, aminanmu na Afirka ne suka shigar da mu cikin MDD. A cikin kasashen mambobin MDD, akwai kasashen Afirka har 53, wadanda suka dau kashi 28% na kujerun babban taron MDD. A kan batun Taiwan da na hakkin bil Adama, haka kuma a kokarin da kasar Sin ta yi na neman iznin shirya wasannin Olympics da bikin baje kolin duniya da dai sauransu, kasashen Afirka sun nuna wa kasar Sin goyon baya sosai.

Bunkasuwar kasar Sin cikin lumana ta kuma bai wa jama'ar Afirka kwarin gwiwa da kuma dabaru. Masu hangen nesa da yawa na Afirka sun gane cewa, dabarun kasar Sin suna da daraja ta musamman. Wani shahararren masanin kasar Nijeriya ya rubuta cewa, 'mun ga kwaskwarima da aka yi a kan tattalin arzikin kasar Sin, wannan abin al'ajabi ya bayyana mana nasarar da wata al'ummar da ke da kwarin gwiwa da niyya da hangen nesa za ta iya samu. Shugaban kasar Angola shi ma ya ce, 'matsayin da kasar Sin ta dauka ya dace da bunkasuwar Afirka. Kasar Sin ta bai wa Afirka taimako, kuma ta kulla hulda irin na inganta hadin gwiwar taimakon juna a tsakaninta da Afirka.'

Yayin da take samun karbuwa sosai a Afirka, kasar Sin ta kuma jawo shakka da kishi daga kasashen yammacin duniya da yawa. Sun ce wai, kasar Sin tana kwace wa Afirka makamashi, tana kafa sabon mulkin mallaka. A cikin labaransu, wasu kafofin yada labarai na kasashen Amurka da Faransa da Japan da dai sauransu sun kuma ce, kasar Sin tana 'yaki da tasirin Amurka a kan Afirka', kuma 'tana kokarin mallakar Afirka' da dai sauransu.

Wadannan bayanai dai sun saba wa tarihi, haka kuma sun gurbata gaskiya. Alal misali, a cikin shekarun baya, kasar Sin ta kara karfin shigowa da kayayyaki daga Afirka. Yawan cinikin da aka yi tsakanin Sin da Afirka ya kai dallar Amurka biliyan 39.8 a shekara ta 2005, daga cikinsu yawan kayayyakin da kasar Sin ta shigo daga Afirka ya kai biliyan 21.1, wanda ya zarce yawan kayayyakin da take fitarwa zuwa Afirka. bayan haka kuma, matakai da dama da kasar Sin ta dauka sun amfana wa bunkasuwar Afirka. kamar misali, tun daga watan Janairu na shekarar da muke ciki, kasar Sin ta soke kudin kwastan a kan kayayyaki 190 na kasashen Afirka 30 wadanda suka fi rashin samun cigaba. Sakamakon hakan dai, yawan kayayyakin nan da wadannan kasashe suka fitar zuwa kasar Sin ya karu har da sau daya.

Kasar Sin kasa mai tasowa mafi girma ce a duniya, kuma Afirka nahiya ce da aka fi samun kasashe masu tasowa. Kasashen Sin da Afirka suna taimakon juna sosai a fannin tattalin arziki, kuma sun kasance da makoma mai kyau a hadin gwiwar da ke tsakaninsu. Babu abin da zai iya dakatar da sahihiyar hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka. Bangarorin Sin da Afirka za su ci gaba da inganta yanayi mai kyau na yin abuta da juna da zaman daidaici da moriyar juna da hadin gwiwa da juna da suke ciki. (Lubabatu Lei)