Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-13 20:36:16    
A sa kaimi ga kyautata tsarin masana'antu da hawan matakinsa

cri

"Tsarin ka'idoji na shiri na 11 na shekaru 5-5 na raya tattalin arzikin kasa da zaman al'umma" na kasar Sin ya gabatar da cewa, ya kamata a mai da aikin kara karfin kirkire-kirkire cikin 'yanci a matsayin farko, a daidaita da kuma kyautata tsarin kayayyaki da na kungiyoyin masana'antu da tsarin kafa sana'o'I, da daga matsayin fasaha da kara karfin yin gasa daga duk fannoni.

"Tsarin ka'idojin" ya nemi da a kara juya hankali daga muhimman sana'o'in yin gyare-gyare da harkada kayayyaki zuwa sana'o'in fitar da kayayyakin da kasarmu ita da kanta ta yi bincike da kera su da kuma hada su, da sa kaimi ga mai da sakamakon da aka samu wajen ayyukan kirkire-kirkire cikin 'yanci za su zama sana'o'in da ke da karfin yin gasa, da wasu muhimman wuraren tafiyar da sana'o'i masu amfani, da wasu masana'antu masu fasahar zamani da wasu shahararrun tamburan kayayyakin da ke da ikon mallakar fasaha.

Ya kamata a daga matsayin sana'ar kera kayayyakin lantarki da sadarwa, da ba da taimako ga sana'ar yin binciken abubuwa masu rai, da yin kokarin samun babban ci gaba wajen muhimmiyar fasaha, da yin binciken muhimman kayayyakin wannan sana'a, da sa kaimi ga bunkasa sana'ar zirga-zirgar jiragen sama da kumbo da sana'ar yin sabbin kayayyaki.

"Tsarin ka'idojin" ya gabatar da cewa, ya kamata a yi kokarin samun babban ci gaba wajen muhimmiyar fasaha, da daga matsayin bincike da tsara fasalin muhimman kayayyaki da kerasu da kuma hada su wajen fasaha. Ya kamata a kara karfin yin kirkire-kirkire cikin 'yanci wajen masana'antar kera motoci, da yada amfanin masana'antu masu ginshiki, da kara yawan rabon tamburan motocin da ke da ikon mallakar fasaha cikin kasuwanni, da hammantar da mutane da su yi amfani da motoci masu tsimin makamashi da kiyaye muhalli da yin amfani da sabbin abubuwan konawa.

Ya kamata a kara bunkasa masana'antar kera jiragen ruwa, da kara kwarewa wajen tsara fasalin manyan jiragen ruwa da hada su da kuma kera su cikin 'yanci.

"Tsarin ka'idojin" ya gabatar da cewa, ya kamata a kafa tsari mai inganci kuma cikin tsimi da tsabta kuma cikin kwanciyar hankali. Bunkasa masana'antar hakar kwal da gawayi ta tsararriyar hanya, da kafa wasu masana'antun wadanda suke iya fitar da kwal da yawansu ya kai Ton miliyan 100. A yi kokarin bunkasa masana'antar ba da wutar lantarki, a kama gaba wajen bunkasa masana'antar ba da wutar lantarki da karfin wuta wadda aka hada manyan Janaretoci masu amfani kuma masu kiyaye muhalli a muhimmin matsayi.

Za a kara bunkasa masana'antar hakar man fetur da isakar gas da sauri, da kara yin gyare-gyaren tsoffin filayen hakar man fetur. Kuma za a kara rubanya kokari don bunkasa makamashin bola jari, da kafa manyan tashoshi guda 30 masu ba da wutar lantarki da karfin isaka wadanda kuma ke iya samar da wutar lantarkin da karfinsa ya kai fiye da kilowatta dubu 100.

"Tsarin ka'idojin" ya gabatar da cewa, ya kamata a mai da aikin bunkasa masana'antar narka karafa a matsayi mai fifiko, da daidaita tsarin barbazuwar masana'antar harhada magunguna, da kawar da masana'antu masu kazantarwa sosai. A sa kaimi ga bunkasa sana'ar yin kayayyakin gine-gine, da sanya babban kokarin fitar da sabbin kayayyakin gine-gine masu tsimin makamashi da kiyaye muhalli.