Ran 12 ga wata a Paris, an yi taron ministocin harkokin waje na kasashen Amurka, Rasha, Sin, Birtaniya, Faransa da Jamus, kuma an tsai da kudurin sake gabatar da matsalar nukiliyar kasar Iran ga kwamitin sulhu na MDD.
Bayan taron, Mr. Douste ? Blazy ministan harkokin waje na kasar Faransa ya karanta wata sanarwa cewa, kasashen 6 za su yi kokari don neman zartar da wani kuduri a kwamitin sulhu, ta haka zai sa hukumar makamashin nukiliyar kasashen duniya ta taka rawa yadda ya kamata. Idan kasar Iran ta ki yarda da wannan kuduri, za su dauki matakai bisa tsarin dokokin MDD.
Mr. Zhang Yesui mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin wanda ya halarci taron ya ce, kullum kasar Sin tana yaki da yaduwar manyan makaman kare dangi, tana ganin cwea yin shawarwarin diplomsiya wata kyakkyawar hanya ce da ake bi wajen warware matsalar nukiliyar Iran cikin lumana. Tana fata bangarorin da abin ya shafa su yi kokari tare don mayar da shawarwari bisa shirye-shiryen warware matsalar nan.
|