An bude dandalin tattaunawa na uku tsakanin shugabannin jami'o'i da kolejoji na gida da na waje a ran 12 ga watan da muke ciki a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin. An labarta, cewa a 'yan shekarun baya dai, kasar Sin ta yi namijin kokari wajen yin hadin gwiwa da musanye-musanya tsakaninta da kasashen ketare a fannin ba da ilmi a jami'o'i da kolejoji na kasar. Hukumomin ba da ilmi na kasashen ketare suna masu sha'awar mayar da jami'o'i da kolejoji na kasar Sin a matsayin abokansu na hada kai.
Jami'ar horar da malamai ta Beijing ita ce daya dake cikin shahararrun jami'o'in kasar Sin. A 'yan shekarun baya, wannan jami'a ta mayar da aikin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a matsayin wani muhimmin aiki na yalwatuwa. Yanzu, wannan jami'a ta rigaya ta kulla kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa da musanye-musanye tare da jami'o'i da kolejoji da kuma kungiyoyin kasa da kasa na kasashe da jihohi fiye da 40 na duniya. Kuma yawan dalibai na jami'ar ya zarce 1,700. Shugaban wannan jami'a Mr. Zhong Binglin ya furta, cewa:
'Lokacin da muke yin hadin gwiwa da musanye-musanye tare da kasashen ketare, mukan yi koyi da hasashe da kuma dabaru na zamani da kasashen waje suke da su wajen ba da ilmi ; daga baya mu yi gyare-gyare da aikin bunkasa jami'ar bisa hakikanin halin da ake ciki a jami'o'i da kolejoji na kasar Sin ; Yin haka, ya janyo babbar moriya gare mu wajen yin nazari ta fuskar kimiyya da kuma horon kwararun mutane da kuma kara yin suna a duniya'.
An labarta ,cewa jami'o'i da kolejoji ciki har da jami'ar Beijing da jami'ar Qinghua yanzu suna nan suna himmantuwa wajen yin hadin gwiwa tare da kasashen waje. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, kasar Sin ta riga ta kafa dangantakar hadin gwiwa tsakaninta da kasashe da jihohi 178 a fannin ilmantarwa.
Jama'a masu sauraro, ko kun san cewa, tun dogon lokaci ne gwamnatin kasar Sin take dukufa wajen kafawa da kuma kyautata tsarin ba a ilmi a jami'o'i da kolejoji. Yawan jami'o'i da kolejoji da take da su sun karu zuwa sama da 2,000 daga 200 kawai da aka kafa tsakanin shekarar 1950 zuwa 1959. Abun farin ciki, shi ne dimbin hukumomin ba da ilmi na kasashen waje sun mayar da jami'o'i da kolejoji na kasar Sin a matsayin manyan abokansu na hadin kai. Kolejin fasaha ta sarautar Stockholm yana daya daga cikinsu. Shugaban kolejin nan Mr.Anders Flodstrom ya fadi, cewa : 'Mun yi hadin gwiwa tare da jami'o'i da kolejoji da yawa na kasar Sin. Ta wannan hanya ce muka samu abubuwa da dama. Na yi imanin, cewa nan gaba akwai dalibai mafi yawa na kasar Sin da za su zo nan kasar Swaden domin yin dalibta ; haka kuma dalibai na kasarmu za su je kasar Sin domin yin dalibta'.
An kuma labarta, cewa shugabannin jami'o'i da na kolejoji daga kasashen Amurka da kuma Faransa da dai sauransu su ma sun bayyana kyakkyawan burinsu na kara yin hadin gwiwa tare da jami'o'i da kolejoji na bangaren kasar Sin.
Wakiliyar majalisar gudanarwa ta kasar Sin Madam Chen Zhili ta yi jawabi a gun bikin bude dandalin tattaunawar, inda ta furta, cewa :
'Saboda kasarmu tana bayan kasashen duniya a zahiri a fannin kimiya da fasaha, don haka, wata hanyar da ta fi dacewa da mu, ita ce bude kofa ga kasashen ketare domin horar da wassu kwararrun mutane da za su cimma matsayin duniya a fannin kimiyya da fasaha. Wajibi ne mu nace ga bin manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje ,da sa kaimi ga mazanartan kimiyya da fasaha da kuma kafa cibiyoyin nazari na zamani.'
Jama'a masu sauraro, mun samu labarin, cewa tun daga shekarar 1950 na karnin da ya wuce, gwamnatin kasar Sin ta samar da kudin bonas ga dalibai Afrikawa dake yin dalibta a nan kasar Sin, wadanda yawansu ya dara 20,000 ; Kazalika, ta aika da malamai fiye da 500 na sana'o'in musamman zuwa Nahiyar Afrika domin tallafa wa kasashen Nahiyar wajen bunkasa kimiyya da fasaha. ( Sani Wang )
|