Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-12 20:55:22    
Maganin gargajiya na kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Hajiya Aisha Habibu mai goro daga Zaria jihar Kaduna, arewacin tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ta rubuto mana, ta ce, na ji an ce maganin gargajiya na kasar Sin na da amfani mai ban mamaki, ko za ku ba mu bayani dangane da maganin gargajiya na kasar Sin. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani a kan maganin gargajiya na kasar Sin.

Kasar Sin tana daya daga cikin kasashen da suka fi dadadden tarihi a duniya, kuma ta yi arziki a fannin kimiyya da al'adu. Likitancin gargajiya da maganin gargajiya na kasar Sin suna kuma daya daga cikinsu.

Bisa takardun tarihi, an ce, tuni a shekaru fiye da 3000 da suka wuce, Sinawa sun fara yin amfani da maganin gargajiya na kasar Sin wajen yaki da cututtuka iri daban daban. A shekaru aru aru da suka wuce, mutanen Sin sun rayu bisa kamun kifi da farauta, kuma suna dibar 'ya'yan itatuwa da tsire-tsire domin su ci. Bayan da suka ci wadannan abubuwa, sai su kan gane cewa, abubuwa iri daban daban suna da amfani daban daban ga jikin dan Adam. A cikin lokaci mai tsawo, sannu a hankali ne suka fara samun ilmi da kuma fasaha dangane da yadda za a bambanta amfanin wadannan tsire-tsire, kuma suka fara yin amfani da su a fannin jiyya da kiwon lafiya. A kai a kai kuma, wadannan tsire-tsire sun zama magunguna. Wannan shi ne asalin maganin gargajiya na kasar Sin.

Sabo da kasar Sin tana da fadi sosai, shi ya sa tana da arzikin magungunan sha na gargajiya masu yawa. Ya zuwa yanzu dai, yawan magungunan gargajiyar kasar Sin da aka gano ya riga ya kai sama da dubu 5.

Magungunan gargajiyar kasar Sin sun yi yawa, kuma a kan bi hanyar musamman wajen yin maganin. Ko wane irin maganin kuma, ya kan hada da tsire-tsire fiye da goma. Wasu ana yin su cikin kwayoyi, wasu kuwa ana tafasa su a cikin ruwa, sa'an nan a sha ruwan. Magungunan gargajiyar kasar Sin suna da amfani mai kyau, kuma yawanci ba su da illa sosai. Bisa nazarin da aka yi kuma, an ce, magungunan gargajiya na kasar Sin suna da amfanin musamman ga wasu cututtuka masu tsanani wadanda ake shan wahalarsu har ma a zamanin yanzu.

A nan kasar Sin, akwai shahararrun masana'antun maganin gargajiya masu yawa, kuma ana sayar da magungunan da suke masana'anta har zuwa kasashen kudu maso gabashin Asiya da kuma kasashen Turai da Amurka da dai sauransu. Tuni a karni na biyu kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam, an riga an shigar da wani maganin gargajiya da ake kira Dahuang wanda ake iya samunsa musamman ma a kasar Sin cikin Turai. A shekaru fiye da 1300 da suka wuce kuma, masanan ilmin maganin gargajiyar kasar Sin sun sa sawunsu har zuwa kudu maso gabashin Asiya don ilmantar da jama'a a kan ilmin magani, sun kuma tafi tare da likitanci da maganin gargajiya na kasar Sin.

Bisa nazarin da za a kara yi a kansa, maganin gargajiyar kasar Sin zai kara yaduwa a duk fadin duniya, kuma zai kara taka gaggarumar rawa a wajen taimaka wa dan Adam yaki da cututtuka iri iri.

To, masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen bayanin da muka yi dangane da maganin gargajiyar kasar Sin. Tare da fatan kun ji dadin bayanin, kuma za ku ci gaba da rubuto mana wasiku da kuma sauraron shirinmu na amsoshin wasikunku, ni Lubabatu da na gabatar daga nan Beijing ke cewa, sai mako mai zuwa, idan Allah ya kai mu.(Lubabatu Lei)