Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-12 17:42:36    
Jam'iyyun dimokuradiyya da mutane da ba 'yan jam'iyya ba suna taka rawa sosai wajen shiga harkokin mulki a kasar Sin

cri

Jam'iyyar Kwaminis ta Sin jam'iyya ce da ke rike da mulkin kasar Sin. A lokacin da ake jagoranci jama'ar Sin ga raya kasar, ko da yaushe kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin yana mai da hankali ga barin jam'iyyun dimokuradiyya da shahararrun mutane da ba 'yan jam'iyya ba da su taka rawarsu wajen shiga harkokin mulki a kasar Sin.

Shehun malami Chen Junliang, mai shekaru sama da 70 da haihuwa a bana, shi ne mamban cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin da na cibiyar aikin injiniya ta kasar, kuma yana daya daga cikin shahararrun masanan kimiyya na kasar Sin a fannin sadarwa. Shehun malami Chen Junlinag, ba dan jam'iyya ba ne. Yanzu ya zama mamban zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, kuma ya taba zama dan majalisar wakilan jama'ar kasar. Da ya waiwayo hanyar da ya bi wajen shiga harkokin mulkin kasa a cikin sama da shekaru 10 da suka wuce, ya bayyana cewa, "a shekarar 1997, gwamnatin kasar Sin ta shirya mambobin cibiyar nazarin kimiyya ta kasar wadanda ba 'yan jam'iyya ba da suka yi rangadin aiki a lardin Shandong. Makasudin rangadin aikin shi ne domin sanya mambobin su fahimci halin da ake ciki dangane da kwaskwarima da aka fara yi kan shirin tsarin hannun jari ba da dadewa ba a wancan lokaci. Ta hanyar, ba ma kawai mun fahimci halin da ake ciki a lardin Shandong ba, har ma mun fahimci abubuwa a kan yadda ake yin kwarskwarima a kan shirin tsarin hannun jari a wasu masana'antu. "

Ma'aikatar kula da harkokin hadin kai ta kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta kan shiryawa 'yan jam'iyyun dimokuradiyya da shahararrun mutane da ba 'yan jam'iyya ba, da su yi rangadin aiki kan manyan batutuwan kasa a wurare daban daban, ta yadda za su iya gabatar da ra'ayoyinsu da shawarwarinsu a kan harkokin mulki. Kuma an sami sakamako mai kyau wajen yin hadin guiwa a tsakanin jam'iyyun siyasa.

Shehun malami Chen Junliang ya kara da cewa, "yawan 'yan Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ya kai miliyan 70 a yanzu. Yawancinsu nagargarun mutane ne a kasarmu. Amma akwai nagargarun mutane da yawa wadanda ba 'yan Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ba ne, wasu daga cikinsu 'yan jam'iyyun dimokuradiyya ne, wasunsu kuwa ba 'yan jam'iyya ba ne. Ya kamata, a ba wadannan nagargarun mutane kwarin guiwa ta yadda za su yi kokari wajen neman cim ma manufar kasarmu tare."

A kwanakin baya, Madam Liu Yandong, mataimakiyar shugabar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin kuma ministar ma'aikatar kula da harkokin hadin kai ta kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta bayyana cewa, jam'iyyun dimokuradiyya da shahararrun mutane da ba 'yan jam'iyya ba wadanda suka kware wajen shiga harkokin mulki suna ba da taimako wajen kyautata babban tsarin harkokin siyasa na kasa da gudanar da harkokin zamantakewar al'umma yadda ya kamata. Ta ce, "daga cikin 'yan majalisun wakilan jama'a na mataki daban daban na kasar Sin, akwai 'yan jam'iyyun dimokuradiyya da shahararrun mutane da ba 'yan jam'iyya ba wadanda yawansu ya kai dubu 170, ka zalika daga cikin majalisun ba da shawara kan harkokin siyasa na matakai daban daban, akwai su da yawansu ya kai dubu 330. Wadannan 'yan majalisu wadanda suka kware wajen shiga harkokin mulki suna ba da babban taimako ga kyautata babban tsarin siyasa na kasa da kara karfin hadin kai a tsakanin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da mutanen bangarori daban daban." (Halilu)