Chengjisihan na daular Mongoliya da aka kafa a karni na 13 shi ne wani mashahurin mutum ne a tarihin kasar Sin. A duk rayuwarsa, ya ba da gudumuwa sosai ga kafa da yalwata kabilar Mongoliya. Shugaba Mao Tsedong wanda ya kafa sabuwar kasar Sin wato Jamhuriyar jama'ar Sin ya taba rubuta wata waka wadda a ciki ya nuna masa yabo cewa, jarumin da aka samu daga sararin samaniya, amma a tsakanin jama'a, ana yadadda labaru dangane da Chengjisihan a ko'ina a kasar Sin.
Ma'anar Chenjisihan ita ce sarkin da ya yi girma sosai tamkar yadda teku ya ke, sunansa na ainihi shi ne Tiemuzhen. An haife shi a wani gidan babban mutum a shekarar 1162. A makiyayyar Mongoliya ta karni ta 12, wata tsohuwar kabila ce da ta yi mulki a rukuni rukuni, kuma an nuna karfin tuwo da yake-yake da kwace-kwace a ko'ina . A lokacin da yake karami, an kashe mahaifinsa, 'yan rukunin kabilarsa sun watsu. Tiemuzhen da ke da shekaru 10 da haihuwa ya yi fama da talauci sosai tare da mahaifiyarsa da kannensa, sauran 'yan rukuni daban sun taba kama shi, sa'anan ya tsirar da kansa, ya shiga cikin wani rukuni daban da ke da karfi sosai. A lokacin da ya balaga, an kuma kama matarsa, bayan da ya ci nasarar yakin, sai ya sake dawo da matarsa.
A lokutan da ya kan fuskanci samame da kirarin kisa da aka yi masa , Tiemuzhen ya kara kwarewa ya zama mutumin da ya fi sauran mutane wajen samun hazikanci da ingancin niyya. A fuska, ya yi abubuwa tamkar yadda ya bi sawun rukunin da ke da karfi sosai, amma a hakika ya biya bukatun sauran mutane a boye ya nemi kauna daga wajensu, ya tattara sojoji da dawaki da yawa, ya raya karfinsa na kansa a boye. A lokacin da ya cika shekaru 27 da haihuwa, ya kafa rukunin kabilarsa, ya zama sarkin rukunin, wato 'Han" ke nan. A cikin shekaru fiye da goma da suka wuce, ya kafa rundunar sojojin da ke da karfi sosai a makiyayyar Mongoliya, wato ya kafa babbar kasar Mongoliya, daga nan aka soma kiransa da cewar "Chengjisihan".
Bayan da Chengjisihan ya kafa kasar Mongoliya, ya tabbatar da tsarin mayar da mulkin kasa a cikin hannun mutum daya, ya kago kalmomin kabilar Mongoliya, ana amfani da kalmomin nan har zuwa yanzu.
A wancan lokacin, a kasar Sin , ban da mulkin kabilar Han da ke da shekaru fiye da dubu, sai aka samu mulkin sauran kananan kabilu, kamar su daular Liao da Xia ta yamma da Jin da dai sauransu. Chengjisihan ya kara karfinsa, ya kwace dukiyoyi, ya yi yaki da wadannan dauloli, ya yi ta samun nasara, a kai a kai ne ya kara habaka iyakar kasar Mongoliya . A shekarar 1219, Chenjisihan ya soma yaki a babbar nahiyar Asiya da ta Turai, saboda haka, ya dakatar da bunkasuwar da aka samu a shiyyar Asiya da shiyyar gabashin Turai a wani lokaci.
Amma, bisa habakawar da ya samu wajen soja, an kara yin ma'amalar al'adu da tattalin arziki a tsakanin shiyyar gabas da yamma na duniya. A lokacin da sojojin Mongoliya suka yi yake-yake, suna kan shimfida hanyoyin zirga-zirga da kuma gina gadoji a kan koguna, shi ya sa sun kyautata sharudan zirga-zirga a tsakanin gabas da yamma na duniya, a kan manyan hanyoyin zirga-zirga, sojojin Mongoliya sun kafa tashoshi masu aikin gadin hanyoyin da kuma bayar da umurnin kiyaye lafiyar 'yan kasuwa a kan hanyoyin kai da kawowa.
A shekarar 1227, Chengjisihan da ke da shekaru 65 ya mutu bisa sakamakon kamuwa da ciwo a kan hanyar yeke-yake.
Chengjisihan ya kafa kasar Mongoliya da ke hada da nahiyar Asiya da nahiyar Turai. A shekarar 1279, jikansa mai suna Hubilie ya hallaka daular Son ya kafa daular Yuan. (Halima)
|