Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-12 16:11:02    
Jamhuriyar Ghana

cri

Assalamu alaikun , Jama'a masu sauraro, barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jinni wato shirinmu na "Yawon shakatawa a kasashen Duniya ". A cikin shirinmu na yau za mu karanta muku wani bayani mai lakabin haka: An kai ziyara a Jamhuriyar kasar Ghana .

Jama'a masu sauraro, Jamhuriyar Ghana tana yammacin Afrika ne kuma tana gabar arewacin Gulf Guinea . A yamma tana hade da kasar Kwat Dibwa. A arewa tana iyaka da kasar Burki Nafaso . A gabas tana makwabtaka da kasar Togo . A kudu tana fuskantar Tekun Atlantic . Kasar Ghana ba kawai tana fitar da koko ba har ma tana fitar da zinariya .

Fadin yankin kasar Ghana ya kai muraba'in kilomita dubu 238 da dari 5 . Yawan mutanen kasar ya kai miliyan 21. Galibin mutanen kasar suna bin addinin Krista da tsohon addini na gargajiya da musulunci . Turanci ya zama harshen gwamnati na kasar Ghana.

A shekarar 1897 , kasar Ingila ta kai hari a Ghana kuma ya yi mulkin malla a yankin . Saboda kasar tana fitar da zinariya , shi ya sa 'yan mulkin mallaka sun ba sunan Gold Coast ga kasar . A ran 6 ga watan Maris na shekarar 1957 , kasar Gold Coast ta sanar da samun mulkin kai kuma ta sauya sunan kasar zuwa Ghana .

A ran 1 ga watan Yuli na shekarar 1960 , an kafa Jamhuriyar Ghana , amma tana cikin Kungiyar kasashen Renon Ingila wato Commonwealth .

Kasar Ghana tana da wadatun albarkatu . Yawan ma'adinan zinariya da lu'u lu'ai da sauran 'karfe da ba safai ake ganinsu ba ya kai matsayin gaba a duniya . Yawan yankin da kurmi ke mamaye a Ghana ya kai kashi 34 cikin 100 na duk fadin kasar . Zinariya da Koko da katako kayayyakin gargajiya ne da kasar take fitar da su zuwa kasashen waje . Tattalin arzikin kasar Ghana yana dogara bisa wadannan kayayyakin .

Kasar Ghana tana fitar da koko mai yawa . Kasar kasa ce mafi girma a duniya a wajen fitar da koko . Yawan koko na kasar ya kai kashi 13 cikin 100 na jimlar koko na duniya .

A cikin aikin noma na kasar Ghana akwai masar da dankali da dawa da shinkafa da gero da sauransu. Daga cikin irin amfanin gonar da ake sanyawa a kasar Ghana akwai auduga da roba da gyada da kwakwa da rake da ganyen taba .

Tun daga shekarar 1983 kasar Ghana ta fara yin gyare-gyaren tattalin arziki , kullum tana kiyaye yukurin karuwar arziki. A shekarar 1994 , Majalisar Dinkin Duniya ta soke sunan Ghana daga kasashe mafi talauci a duniya.

A ran 5 ga watan Yuli na shekarar 1960, kasar Sin da kasar Ghana sun kulla huldar diflomasiya . Bayan haka shugabannin kasashen biyu sun yi masanya ziyara ga juna sau dayawa . Huldar hadin kai a wajen siyasa da tattalin arziki ta sami yalwatuwa sosai .

To, jama'a masu sauraro , shirin"Yawon shakatawa a kasar Sin " da za mu iya kawo muku ke nan a yau . Ado ne ya shirya wannan shirin kuma ya fasara wannan bayanin, Lawal ne ya karanto muku . Da haka muke muku sallama tare da fatan alheri . (Ado)