Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-12 14:08:04    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (06/07-12/07)

cri

An yi gasar karshe ta cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta Jamus a shekarar 2006 a ran 9 ga watan nan, agogon wurin, inda kungiyar Italiya ta lallasa ta Faransa da ci biyar da uku bayan da suka buga fanarite da juna. Wannan nasara da Italiya ta samu, ita ce ta hudu da ta sami damar daukar kofin duniya. Ga Faransa kuwa, babu abin da ya rage mata, sai kasance da matsayi na biyu. Ban da wannan kuma, kasar Jamus wato mai masaukin baki ta lashe ta Portugal da ci uku da daya a gun gasar karshe da aka gudanar kafin wannan lokaci, wato ke nan ta samu lambar taglla.

A gun wasan tsakanin mata biyu-biyu na budaddiyar gaar wasan kwallon tennis da aka kawo karshenta a ran 9 ga watan nan, agogon wurin a Wimbledon na kasar Burtaniya, 'yan wasa su Zhenjie da Yanzi na kasar Sin sun lallasa abokan karawarsu da ci biyu da daya , wato ke nan sun dauko kofin zakaran Wimbledon ga kasar Sin a karo a farko, kuma wannan kofi na biyu ne na kasaitacciyar gasar wasan kwallon tennis da aka yi a kasar Australiya a farkon shekarar da muke ciki. A gasar tsakanin namiji da namiji, Sannannen dan wasa mai suna Roger Federer daga kasar Swiss ya lallasa abokin karawarsa mai suna Rafael Nadal daga kasar Spain, wato ke nan ya zama lambawan cikin shekaru hudu a jere a gasar wasan kwallon tennis na Wimbledon; Ban da wannan kuma, 'yar wasa mai suna Amelie Mauresmo daga kasar Faransa ta lashe abokiya karawarta mai suna Justine Henin daga kasar Belgium, wato ke nan ta zama zakara a gun gasar.

An yi hadaddiyar gasar zinariya ta zango na biyu ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasa da kasa a ran 8 ga watan da muke ciki a Paris na kasar Faransa. Dan wasa mai suna Liu Xiang na kasar Sin ya zo na hudu a cikin gasar gudun tsallake shinge na tsawon mita 110 na maza da dakika 13 da digo 19. Dan wasa mai suna Terrence Rrammell daga kasar Amurka ya zama zakara a gun gasar. ( Sani Wang )